Yan Sanda Sun Gayyaci Mutum 5 Kan Mutumin Da Ake Rufe Tsirara Na Fiye Da Shekaru 20 A Kaduna

Yan Sanda Sun Gayyaci Mutum 5 Kan Mutumin Da Ake Rufe Tsirara Na Fiye Da Shekaru 20 A Kaduna

  • Yan sanda a Kaduna sun gayyaci mutane biyar domin taimaka musu da bincike kan mutumin da aka gano an rufe a daki
  • A ranar Laraba ne rundunar yan sandan suka ceto mutumin a wani gida da ke Bayajida cikin daki da ake ce an rufe shi kimanin shekaru 20
  • Yan sandan sun ce binciken da suka fara ya nuna mutumin yana da mata da yara amma a halin yanzu ba a san inda suka tafi ba

Kaduna - Rundunar yan sanda a Kaduna ta gayyaci wasu mutum biyar don taimaka mata a binciken da ta ke yi kan rufe wani mutum dan shekara 67 a na tsawon shekaru 20 a Kaduna.

Kakakin yan sanda DSP Muhammad Jalige, ya bayyana hakan a ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu Hausawa sun yi mummunan hadari a Enugu, da yawa sun kone kurmus

Yan Sandan Kaduna
Yan Sanda Sun Gayyaci Mutum 5 Kan Mutumin Da Ake Rufe Na Fiye Da Shekaru 20 A Kaduna. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ceto mutumin, Mr Ibrahim Ado, ne a wani gida da aka rufe shi a Bayajiadda/Ibrahim Taiwo Road, karamar hukumar Kaduna ta Arewa a ranar Laraba.

Jalige ya fada wa manema labarai cewa ma'aikatan duba gari da ke aiki a Bayajiadda by Ibrahim Taiwo Road a Kaduna ne suka kai rahoto.

A cewarsa, bayan samun rahoton, kwamishinan yan sandan Kaduna, Yekini Ayoku, ya tura mutane zuwa wurin suka fito da mutumin.

Ya ce kwamishinan ya bada umurnin a bincika dalilin da yasa aka tsare mutumin tsawon lokaci.

Ya ce an rufe mutumin kusan shekaru 20, a can ciki ya ke cin abinci, fitsari da komai.

Ya ce:

"Mun tafi wurin, mun tarar da shi ba tufafi, mun bashi kaya ya saka kuma muka fito da shi muka kai shi asibiti a duba shi."

Kara karanta wannan

Wata Fatima Abubakar Ta Zuba Wa Mijinta Guba a Abinci, Tace Ta Tsani Aure a Rayuwarta

Jalige ya kara da cewa kwamishinan yan sandan na Kaduna ya kuma bada umurnin yin sahihin bincike don gano ainihin dalilin da yasa aka yi wa dattijon irin wannan rashin tausayin.

Ya ce DPO na ofishin yan sanda na Magajin Gari ya fara bincike kuma za a gano ainihin abin da ya faru.

Mun samu mutum 5 da ke taimaka mana - Jalige

Ya ce sun samu wasu mutane biyar a unguwar da ke taimaka musu a binciken da suke yi.

Jalige ya ce:

"An fahimtar da mu cewa mutumin yana da yara da mata amma ba a san inda suka tafi ba, muna kyautata zaton mutanen da muka tarar a gidan da makwabta za su taimaka mana gano ainihin abin da ya faru."
"Za mu yi aiki tare da likitoci domin samun rahoto kan lafiyarsa. Abin da ya fi muhimmanci shine a duba lafiyarsa da bashi kulawa, kuma mun yi nasarar yin hakan."

Kara karanta wannan

Dan a mutun Peter Obi ya samu lambar yabo a kasar Tanzania bayan kafa tura a Kilimanjaro

Wasu sun yi ikirarin mutumin dan uwansu ne

Wata baiwar Allah wacce ta nemi a sakaya sunanta ta tuntubi Legit.ng bayan karanta rahoton, inda ta ce mahaifinta ne kuma asalinsa a Maiduguri ya ke zaune amma ya bar gida tsawon shekaru ana nemansa ba a same shi ba.

Ta ce:

"Mahaifi na ne, a Maiduguri ya ke sai dai tsawon shekaru ya bace, mun yi ta nema ba mu gan shi ba."

Legit.ng ta shawari matar ta tuntubi rundunar yan sandan jihar Kaduna domin samun karin bayani tunda mutumin yana hannunsu.

Mun tafi wuri wurin yan sanda mun duba amma ba mahaifin mu bane, In ji matar

Sai dai bayan yan kwanaki, matar ta sake tuntubar Legit.ng ta ce yan uwanta sun tafi wurin yan sanda sun kuma gano ashe ba mahaifin nasu bane.

Kalamanta:

"Ni ban tafi ba, amma yan uwa na sun tafi wurin yan sandan sun duba amma sun gano ashe ba mahaifin mu bane, muna fatan Allah ya bayyana mana shi."

Kara karanta wannan

Ba Sojojin Amurka Ne Suka Kai Samame A Abuja Ba, In Ji Mazaunin Unguwa

An Gano Wani Mutumi Tsirara Da Aka Kulle a Daki Tsawon Shekara 20 a Kaduna

Tunda farko, kun ji cewa wani bawan Allah da aka garkame tsawon shekara 20 a Layin Benin da ke tsakiyar birnin Kaduna ya shaƙi iskar yanci ta hannun jami'an duba gari ranar Laraba.

Jami'an duba garin da suka samu wannan nasara sun shaida wa jaridar Tribune ranar Laraba cewa sun kaɗu sosai da gano mutumin mai matsakaicin shekaru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel