Jirgin Yakin Sojojin Rasha Ya Yi Hatsari A Kan Gidajen Mutane, An Rasa Rayuwa

Jirgin Yakin Sojojin Rasha Ya Yi Hatsari A Kan Gidajen Mutane, An Rasa Rayuwa

  • Wani Jirgin Yakin sojojin Rasha ya faɗa kan ginin da nutane ke zaune a kudancin birnin Yeysk jim kaɗan ya tashi ranar Litinin
  • Rahotanni sun nuna cewa haɗarin jirgin ya yi ajalin mutane 13 yayin da wasu da dama suka samu raunuka kala daban daban
  • Hukumomi a ƙasar sun bayyana cewa injin Jirgin ne ya kama da wuta kuma ta watsu har zuwa tankin Mai

Wani jirgin yaƙin ƙasar Rasha ya yi hatsari a kan gine-gine da mutane ke rayuwa a kudancin birnin Yeysk jim kaɗan bayan tashinsa daga sansanin Soji ranar Litinin da ta gabata.

Jaridar Vanguard tace hatsarin ya yi ajalin mutane 13 biyo bayan Ibtila'im gobara da ta tashi a ginin sanadiyyar faɗuwar jirgin.

Haɗarin jirgin yakin Rasha.
Jirgin Yakin Sojojin Rasha Ya Yi Hatsari A Kan Gidajen Mutane, An Rasa Rayuwa Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

A ruwayar Retuers, wasu aƙalla mutane 19 sun ji raunuka daban-daban sakamakon hatsarin a Yeysk, wani birni da Rasha ta mamaye a kudancin ƙasar Ukraine.

Kara karanta wannan

2023: Kura Ta Kara Turnuke Wa Atiku, Shugabannin PDP a Wata Jiha Sun Yi Fatali da Sunayen Tawagar Kamfe

Kafar yaɗa labaran rundunar soji Zvezda ta wallafa wani Bidiyo wanda ya nuna yadda jirgin ya fashe yayin da ya tunkari yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Jirgin maƙare yake da muggan makamai amma gwamnan jihar Krasnodar, Veniamin Kondratyev, ya musanta rahotannin.

"Idan har abinda ake faɗa gaskiya ne to da rabin ginin wurin ne kaɗai zai saura," Hukumar yaɗa labarai Rasha (RIA) ta rahoto gwamnan na faɗa wa manema labarai.

Wane hali mutanen wurin suka shiga?

Hatsarin jirgin ya yi sanadin kwashe kusan mazauna wurin 250 ciki har da ƙananan yara 40. A cewar RIA lamarin ya faru ne yayin gwajin ɗaukar horo daga sansanin soji.

Ma'aikatan tsaro tace Matukin Jirgin ya aike da sakon cewa Inji ya kamata da wuta tun farkon tashi, daga nan wutar ta watsu har zuwa Tankin Mai a lokacin ne kuma ya faɗa kan ginin.

Kara karanta wannan

Wani Mutumi Ya Mutu a Ɗakin Hotel Bayan Ya Shiga da Wata Mace Zasu Ji Dadi

A wani labarin kuma Jerin Kasashen Duniya 10 Mafi Adadin Rundunar Soja a Duniya a 2022

Kowace kasa na alfahari da adadin Sojojin da take shi da makamai irinsu bindigogi, tankoki da sauransu.

Yayin da wasu ke tunanin Amurka ta fi kowa karfi, kasar Sin ta zarce mata wata adadin runduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel