Usman Rimi: Dalibin Likitanci Na Ajin Karshe Wanda Ya Fara Sayar Da Abinci Saboda Yajin Aikin ASUU Ya Rasu

Usman Rimi: Dalibin Likitanci Na Ajin Karshe Wanda Ya Fara Sayar Da Abinci Saboda Yajin Aikin ASUU Ya Rasu

An tabbatar da rasuwar Usman Rimi, dalibi mai karatun koyon likitanci da tiyata a Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto, UDUS, wanda ya koma sayar da abinci saboda yajin aikin ASUU.

Bayan yin nasara a sana'ar sayar da abinci a shagon da ya bude a unguwar Diplomat da ke Sokoto, Rimi ya rasu a ranar Laraba, 12 ga watan Oktoba bayan gajeruwar rashin lafiya, Daily Nigerian ta rahoto.

Usman Rimi
Yajin Aikin ASUU: Dalibin Mai Likitanci Da Ke Ajin Karshe Usman Rimi Wanda Ya Fara Sayar Da Abinci Ya Rasu. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: UGC

Daya daga cikin na hannun daman marigayin, shugaban 21st Century Entrepreneur Hub, Umar Idris, ya tabbatar da rasuwarsa a ranar Asabar 15 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Idris, an yi jana'izar Rimi a ranar da ya rasu a karamar hukumar Rimi na jihar Katsina bisa koyarwar addinin musulunci.

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Ta Kashe Saurayinta Da Wuka Cikin Dare Kusa Da Dakin Hotel

Idris ya bayyana cewa marigayi Rimi, wanda shine shugaban 21st Century Entrepreneurs Hub reshen Jihar Katsina ya yi rayuwa ta kankan da kai, jajircewa da aiki tukuru.

Bayan shiga shirin koyar da sana'o'in na Global Entrepreneurship a 2019 da 2020, Rimi na ke kula da taron matasan masu kamfanoni a Katsina, shine taron masu kamfanoni mafi girma a jihar a 2019 da 2020.

Idris ya ce, yayin jagorancin Rimi, 21st Century Entrepreneurs Hub a Katsina ta tallafawa kimanin mata da matasa 1,000 da sana'o'i daban-daban.

Yayin wata hira da ya yi a baya-bayan nan da NAN, matashin mai sayar da abincin ya ce yajin aikin ASUU ne ya bashi damar fara sana'ar.

Ya kara da cewa yayin dokar kulle na COVID-19 ya fara sana'ar sayar da kwai da kaji.

Yadda Yajin Aikin ASUU Ya Maida Dalibin Likitanci Mai Siyar da Abinci a Jihar Sokoto

Usman Abubakar-Rimi, wani dalibin ajin karshe a fannin likitanci a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto (UDUS) ya bayyana yadda ya fara sana'ar abinci a kan saboda tsawaitar yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).

Kara karanta wannan

Mamaki Yayin Da Gwamnatin Buhari Ta Amince EFCC Ta Gurfanar Ta Shahararriyar Sanatan APC A Kotu

Idan baku manta ba, ASUU dai ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun bana, inda ta kora dalibai gidan iyayensu tare da maida su 'yan zaman kashe wando, Daily Trust ta ruwaito.

Abubakar-Rimi ya ce zama bai kama shi ba, domin dole ya nemi abin yi domin kashe lokaci da kuma iya daukar nauyin rayuwa da dai sauran abubuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel