Bayan Auren Mata ta 3 a Makon da Ya Gabata, Ooni na Ife ya Auro Mata ta 4 a Makon nan

Bayan Auren Mata ta 3 a Makon da Ya Gabata, Ooni na Ife ya Auro Mata ta 4 a Makon nan

  • Sarkin Ile-Ife, Oba Enitan Ogunwusi ya aura mata ta hudu a cikin watanni biyu kacal kuma ta tare a fadarsa kamar sauran matan uku da ya auro
  • Basaraken ya aura amarya ta hudun ne mai suna Ashley Adegoke a shagalin bikin da aka yi a gidan iyayenta dake titin Ede a Ile-Ife
  • Ya fara da auren Sarauniya Mariam, Sai Elizabeth inda a makon da ya gabata ya aura Tobi Philips sannan a wannan makon ya aura Ashley Adegoke

Ooni na Ile-Ife, Oba Enitan Oginwusi, Ojaja II ya auro sabuwar mata mai suna Ashley Adegoke inda ya shiga da ita fadarsa a cikin wani kasaitaccen biki.

Ooni of Ife
Bayan Auren Mata ta 3 a Makon da Ya Gabata, Ooni na Ife ya Auro Mata ta 4 a Makon nan. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Auren na zuwa ne bayan makonni da basaraken ya yi wani auren inda ya aura Mariam Anako a wani takaitaccen bikin.

An tattaro cewa, basaraken ya auri Adegoke a ranar Juma’a da ta gabata. Hakazalika an yi auren ne a gidansu amaryar dake titin Olubose kan titin Ede a Ile-Ife.

Kara karanta wannan

"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Dan Jarida Makaho Yayi Tsokaci Kan Aure da rayuwarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ashley tana daya daga cikin matan da basaraken ya aura a cikin kwanakin nan. An tattaro cewa sabuwar amaryar ita ce mata ta hudu da basaraken ya aura bayan auren mata uku a cikin wata biyu.

A rahotannin baya-bayan nan dake ta yawo, a watan Satumban da ya gabata ne Ooni ya aura sarauniya Mariam kuma ta shigo fadar a matsayinta na matarsa ta farko. Daga nan ya aura Sarauniya Elizabeth Ogunwusi inda aka yi baikonsu kwanaki kadan bayan aurensa na farko a Magodo, Legas.

Basaraken ya auri sarauniya Toni Philips a matsayinta na matarsa ta uku a ranar 9 ga watan Oktoba.

Mako daya a tsakani basaraken ya aura sabuwar amarya mai suna Adegoke.

Awanni 24 Bayan Ya Yi Sabuwar Amarya, Ooni Na Ife Zai Sake Yin Wuff Da Wata Kyakkyawar Budurwa

A wani labari na daban, kimanin sa’o’i 24 da yin sabuwar amarya a fadarsa, mai martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, ya kammala shiri tsaf domin sake angwancewa da wata budurwa.

A yammacin ranar Talata ne aka shigar da amarya Olori Mariam Anako, fadar Ile-Ife bayan an kammala duk wasu bukukuwan al'ada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel