Awanni 24 Bayan Ya Yi Sabuwar Amarya, Ooni Na Ife Zai Sake Yin Wuff Da Wata Kyakkyawar Budurwa

Awanni 24 Bayan Ya Yi Sabuwar Amarya, Ooni Na Ife Zai Sake Yin Wuff Da Wata Kyakkyawar Budurwa

  • Ooni na Ife na shirin sake angwancewa da wata budurwa awanni 24 bayan ya auri kyakkyawar amaryarsa Mariam Anako
  • Yayin da shirye-shirye ya kankama, fadar Ile Ife ta tura wata tawaga domin su ziyarci dangin Dr. Elizabeth Opeoluwa Akinmuda
  • Mai shirin zama amaryar ta kasance mazauniyar kasar Scotland kuma haifaffiyar jihar Ondo

Osun - Kimanin sa’o’i 24 da yin sabuwar amarya a fadarsa, mai martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II, ya kammala shiri tsaf domin sake angwancewa da wata budurwa.

A yammacin ranar Talata ne aka shigar da amarya Olori Mariam Anako, fadar Ile-Ife bayan an kammala duk wasu bukukuwan al'ada.

Ooni na Ife
Awanni 24 Bayan Ya Yi Sabuwar Amarya, Ooni Na Ife Zai Sake Yin Wuff Da Wata Kyakkyawar Budurwa Hoto: Ile Ife sons
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta rahoto cewa wata tawaga ta musamman daga fadar Ile-Ife da ke jihar Osun sun ziyarci dangin mai shirin zama amaryar, Dr. Elizabeth Opeoluwa Akinmuda.

Kara karanta wannan

Hotuna Da Bidiyoyi: Ooni Na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, Ya Yi Sabuwar Amarya Ajin Farko

Sun dai hadu da iyayen Elizabeth ne a gidansu da ke yankin Magodo ta jihar Lagas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar majiyoyi ta kusa da fadar, mai shirin zama amaryar ta kasance mazauniyar kasar Scotland kuma haifaffiyar garin Ondo da ke jihar Ondo, shafin LIB ya rahoto.

Basaraken ya yi aure-aure a baya amma duk sun rabu da matayen nashi

Kafin ya zama sarki, ya auri Adebukola Bombata a 2008 amma suka rabu. Bayan nada shi, ya auri haifaffiyar yar jihar Edo Zaynab-Otiti Obanor a 2016 amma watanni 17 kawai suka yi tare sannan suka rabu.

Daga nan sai Ooni ya auri Silekunola a 2018 har suka haifi yaro daya tare kafin rabuwarsu a watan Disamba.

Hotuna Da Bidiyoyi: Ooni Na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, Ya Yi Sabuwar Amarya Ajin Farko

Kara karanta wannan

An Shigar da Kara Domin Hana Kwankwaso da Abokin Takararsa Neman Shugaban Kasa

A baya mun kawo cewa babban basaraken kasar Yarbawa mai daraja ta daya, Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi ya angwance da wata kyakyawar budurwa.

Shafin LIB ya rahoto cewa daraktan labarai na mai martaba Ooni, Moses Olafare ne ya yada hotunan bikin a shafukan soshiyal midiya.

Sunan sabuwar amaryar Olori Mariam Anako kuma an tattaro cewa tun a watan Maris aka fara shirye-shiryen auren. A wannan lokacin ne basaraken ya aika manyan tawaga zuwa gidan amaryar domin su nema masa aurenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel