Kotun Ta Haramta Wa Salisu Kira Ko Haɗuwa Da Bilkisu Bayan An Buƙaci Ya Aure Ta, Amma Ya Ce Bai Shirya Ba
- Kotun Musulunci da ke zamanta a Rigasa Kaduna ta datse alakar soyayya tsakanin wani Saurayi mai suna Salisu da budurwarsa Bilkisu
- Hakan na zuwa ne bayan mahaifiyar Bilkisu ta kai kara kotu cewa Salisu ya auri yarta ko kuma ya dena soyayya da ita
- Salisu ya ce bai shirya aure ba, don haka kotu ta raba soyayyar kuma ta haramta masu kiran Bilkisu a waya ko bin layinsu ballanta zuwa gidansu
Kaduna - Wata kotun shariar musulunci da ke zamanta a Rigasa, jihar Kaduna, ta bada umurnin datse soyayya tsakanin Salisu Salele da Bilkisu Lawal saboda iyayensu ba su amince da soyayyar ba.
Alkalin, Malam Salisu Abubakar-Tureta, ya bada umurin bayan masoyan sun yarda su katse soyayyar nasu a gaban masu kula da su da jagororin unguwa, Nigerian Tribune ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bada umurnin cewa:
"Daga yau, Salisu ba zai rika haduwa ko kiran Bilkisu ba. An haramta masa bi ta layinsu ko tsayawa kusa da gidansu Bilkisu.
"Idan aka gano yana kiranta ko haduwa da ita, za a masa hukuncin da ya dace."
Raliya ta fara neman kotu ta tilasta wa Salisu auren Bilkisu
A cewar kamfanin dillancin labarai na NAN, mahaifiyar Bilkisu, Raliya Lawal, a ranar 24 ga watan Agusta ta shigar da Salisu kara, tana rokon kotu ta tilasta shi ya aure yarta ko ya dena soyayya da ita.
Raliya ta ce unguwarsu daya kuma Salisu na zuwa ganin yarta ba da izininsu ba, bayan an hana shi zuwa sai ya koma kiranta a waya suna haduwa a wurare.
"Bana son ya lalata min tarbiyar ya shi yasa na kawo kara kotu."
Nnamdi Kanu: Majalisar Tsaron Najeriya Ta Yi Karin Haske Kan Shugaban IPOB, Ta Bayyana Mataki Na Gaba
Ban shirya aure ba sai nan da shekara biyu - Salisu
A bangarensa, Salisu ya ce yana son Bilkisu amma ba zai shirya yin aure ba sai nan da shekaru biyu.
Ya ce:
"Ni dalibi ne a daya cikin jami'o'in tarayya kuma ba zan so aure ya kawo min cikas ga karatu ba.
"Kuma bani da sadaki kuma har yanzu a gidan iyaye na na ke zaune."
Kaduna: Alkalin Kotun Shari'a Zai Biya Wa Salele N100,000 Sadaki Don Auren Sahibarsa Bilkisu
A baya, kun ji cewa Alkalin kotun shari'a a Kaduna, Malam Salisu Ababakar-Tureta, a ranar Laraba ya amince zai bada tallafin N100,000 don biya wa wani Salisu Salele sadaki ya auri sahibarsa Bilkisu Lawal.
Ya fada wa Salele ya tafi yayi tunani kan tayin da ya masa sannan ya dawo ya fada wa kotu abin da ya yanke a ranar 6 ga watan Satumba da za a cigaba da shari'a, rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng