Rashin Girmama Buhari: Wadanda Suka fi ki Izza Sun Girmama shi Balle ke, Abba Bichi ga Teni
- ‘Dan shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, Yusuf Magaji Bichi, Abba Bichi, ya caccaki mawakiya Teni kan rashin girmama shugaban kasa Muhammadu Buhari
- ‘Dan kwallon kafan ya alakanta mawakiyar da rashin hankalin da ta nuna da yanayin kibarta inda yace Tuluka ce mara hankali
- Ya ce fitattun ‘yan Najeriya kamar su Ngozi Okonjo Nweala da manyan jami’an gwamnati sun girmama shugaban kasan amma ita kuwa tayi mirsisi
Abba Bichi, ‘dan wasan kwallon kafa kuma ‘dan darakta janar na hukumar tsaro ta farin kaya, Yusuf Magaji Bichi, ya zargi mawakiya Teni kan rashin mutunta shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Daily Trust ta rahoto yadda shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata aka baiwa mutum 447 lambar yabo a Abuja.
Teni tana daya daga cikin wadanda aka karrama kuma ta fito ta karba lambar yabonta daga shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Sai dai yadda ta karba tare da yin gaba babu mutuntawa ya janyo cece-kuce.
A wata wallafar da yayi a Instagram, Bichi ya kwatanta ta da:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Tuluka mara hankali.”
Yayi ikirarin cewa ta ki mutunta shugaban Kasa Muhammadu Buhari koda fitattun ‘yan Najeriya kamar darakta janar ta cibiyar kasuwanci ta duniya, Ngozi Okonjo Nwela da manyan jami’an gwamnati suka rissinawa shugaban kasan kafin karbar lambar yabon.
“Tuluka mara hankali, har Okonjo ta rissinar da kanta domin nuna mutuntawa da girmamawa ga shugaban kasan hakazalika sauran manyan jami’an gwamnati.
“Ke wacece da ba zaki girmama shugaban kasa ba? Wannan abun damuwa ne da takaici. An san Yarabawa da girmama na gaba da su amma abin ya zo kan ki shine ki ka nuna girman ka.”
- Yace.
Mawakiyar Najeriya Ta Ki Shan Hannu Da Buhari Yayin Gabatar Mata Da Lambar Yabo, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce
A wani labari na daban, Jama’a sun yi cece-kuce kan yanayin yadda shahararriyar mawakiyar nan ta Najeriya Teni Apata ta karbi lambar girmamawa ta kasa daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mawakiyar Najeriya Ta Ki Shan Hannu Da Buhari Yayin Gabatar Mata Da Lambar Yabo, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce
Sahara Reporters ta rahoto cewa Teni bata yi sha hannu da shugaban kasar ba balle kuma ta gaishe da shi yayin da ya gabatar mata da lambar yabon.
A ranar Talata, 11 ga watan Oktoba ne shugaba Buhari ya karrama yan Najeriya 447 da lambar yaro a cibiyar taro ta kasa da kasa da ke Abuja.
Asali: Legit.ng