Mawakiyar Najeriya Ta Ki Shan Hannu Da Buhari Yayin Gabatar Mata Da Lambar Yabo, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce

Mawakiyar Najeriya Ta Ki Shan Hannu Da Buhari Yayin Gabatar Mata Da Lambar Yabo, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce

  • Shahararriyar mawakiyar Najeriya, Teni Apata na cikin manyan yan Najeriya da Shugaba Buhari ya karrama da lambar yabo
  • An karrama Teni da lambar girmamawa ta MON, kuma ita da kanta taje ta karbi kayanta
  • Wani bidiyo da ke nuna yanayin da mawakiyar ta karbi lambar yabon nata ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

Abuja - Jama’a sun yi cece-kuce kan yanayin yadda shahararriyar mawakiyar nan ta Najeriya Teni Apata ta karbi lambar girmamawa ta kasa daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sahara Reporters ta rahoto cewa Teni bata yi sha hannu da shugaban kasar ba balle kuma ta gaishe da shi yayin da ya gabatar mata da lambar yabon.

Teni da Buhari
Mawakiyar Najeriya Ta Ki Shan Hannu Da Buhari Yayin Gabatar Mata Da Lambar Yabo, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce Hoto: @tenientertainer
Asali: Instagram

A ranar Talata, 11 ga watan Oktoba ne shugaba Buhari ya karrama yan Najeriya 447 da lambar yaro a cibiyar taro ta kasa da kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE Kacal

A yayin taron, Teni ce mutum guda da aka gani bata baiwa shugaban kasar hannu ko ta gashe shi ba a lokacin da take karbar lambar yabonta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wannan abu da tayi ya haifar da cece-kuce a tsakanin yan Najeriya wadanda suka kalli abun da Teni tayi a matsayin cin mutuncin ofishin shugaban kasa.

Martanin jama’a

Okezie Atami:

“Kin ji kunya Teni..ko me ake kiranki ma! Ke abun kunya ce ga dukkan yan Najeriya da aka yiwa tarbiya mai kyau! Kin kunyata kanki amma ba ofishin shugaban kasa ba, kin taka rawar matasa marasa tarbiya. Kin ji kunya!”

Prettyyetty:

“Ban ga laifinta ba. Wadanda suka sanya sunanta a cikin jerin ne ke da matsala. Wani gudunmawa ta baiwa masana’antar nishadantarwa a inda muke da Dbang da sauransu.”

Vadeboje:

“Bata cancanci lambar yabon ba a janye shi idan da hali, halayyar dan adam na da tasiri sosai. Wannan ragi ne a gareta zata yi danasani a kai.”

Kara karanta wannan

Shekara 2 da Barin Ofis, Magu Ya Bayyana Dalili 1 da Ya sa Aka Fatattake Shi daga EFCC

Kalli bidiyon a kasa:

Kallon Mamakin da Buhari Yayi wa Shigar Ezra Olubi a Wurin Bada Lambar Yabo ya Janyo Cece-kuce

A gefe guda, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya da dama lambar yabo a ranar Talata, 11 ga watan Oktoban 2022.

Daga cikin wadanda suka amshi lambar yabo harda Ezra Olubi, shugaban kamfanin Paystack, wani dandalin biyan kudi na kasa da kasa.

Sai dai kuma, alamu sun nuna Buhari bai yi tsammanin ganin Olubi cikin yanayin shigar da bayyana ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel