An Rasa Ran Mutum 1 a Farmakin da ‘Yan Bindiga Suka kai Maitama Dake Abuja

An Rasa Ran Mutum 1 a Farmakin da ‘Yan Bindiga Suka kai Maitama Dake Abuja

  • Yan bindiga sun kai farmaki titin Gana dake yankin Maitama a babban birnin tarayyar Najeriya dake Abuja
  • Kamar yadda aka gano, miyagun sun harbe mutum daya a kai yayin da yayi kokarin ceto wani wanda suka zo sacewa
  • ‘Yan bindigan sun bayyana a mota baka kirar Prado SUV wacce suka ajiye a kofar wani gida kafin aiwatar da mugun nufinsu

FCT, Abuja - A kalla mutum daya aka bindige yayin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kutsa titin Gana dake yankin Maitama a babban birnin tarayyar Abuja.

Daily Trust ta rahoto cewa, lamarin ya faru ne wurin karfe 8:46 na daren Laraba.

‘Yan Bindiga
An Rasa Ran Mutum 1 a Farmakin da ‘Yan Bindiga Suka kai Maitama Dake Abuja. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Bidiyon malamin makarantan da ya tafi banki da 'Ghana Must Go' don karbo albashinsa

Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a boye sunansa ya sanar da Daily Trust cewa, wanda abun ya ritsa da shi an kashe shi yayin da yake kokarin ceto wani mutum da aka tirsasa cikin wata bakar motar kirar Prado SUV.

Yace an ajiye motar kirar SUV a gida mai lamba 44 kan titin Gana inda aka harbe mutumin a kai kuma ya sheka lahira a take.

Majiyar ta kara da cewa wadanda ake zargin sun tsere da wanda suka sace sannan suka bar gawar wanda suka halaka inda yake kwance a titi har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

Kamar yadda yace, wannan ne karo na biyu da hakan take faruwa a kan titin Gana a cikin makonnin nan.

Mazauna yankin sun ce wasu mutane sun dinga kaiwa da kawowa a yankin, ta yuwu su ke da alhakin harin.

Yace yaran da suka dinga karakaina a yankin sun fi sa ido kan wuraren siyar da magani da manyan kantuna a Maitama, inda ya zargi cewa ‘yan sanda basu yin komai wurin baiwa wuraren tsaro.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: An Gano Wani Bawan Allah Tsirara da Aka Kulle Tsawon Shekara 20 a Kaduna

A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace tuni ‘yan sanda sun bazama neman wadanda suka yi aika-aikar.

Adeh mai mukamin DSP ta musanta zargin da ake yi na cewa ‘yan sanda basu komai wurin tsare yankin.

Sojojin Najeriya Sun Dakile Harin Kwantan Bauna da Boko Haram Suka kai Musu, Sun yi Musu Lugude

A wani labari na daban, Dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Hadin Kai sun dakile wani hari da ‘yan Boko Haram suka kai a Borno, jaridar TheCable ta rahoto.

Harin kwantan baunan da ‘yan ta’addan suka kai an bankado shi yayin da dakarun suka budewa ‘yan ta’addan wuta tsakanin Kumshe da Bama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel