An Gano Wani Mutumi Tsirara Da Aka Kulle a Daki Tsawon Shekara 20 a Kaduna

An Gano Wani Mutumi Tsirara Da Aka Kulle a Daki Tsawon Shekara 20 a Kaduna

  • Jami'an duba gari sun yi nasarar kuɓutar da wani mutumi a Layin Benin dake kwaryar birnin Kaduna ranar Laraba
  • Bayanai sun nuna cewa mutumin mai matsakaicin shekaru ya kwashe shekara 20 a kulle komai na rayuwa a ɗakin yake yi
  • Tuni dai jami'an yan sanda suka isa wurin suka tafi da mutumin, har yanzun babu sanarwa a hukumance

Kaduna - Wani bawan Allah da aka garkame tsawon shekara 20 a Layin Benin da ke tsakiyar birnin Kaduna ya shaƙi iskar yanci ta hannun jami'an duba gari ranar Laraba.

Jami'an duba garin da suka samu wannan nasara sun shaida wa jaridar Tribune ranar Laraba cewa sun kaɗu sosai da gano mutumin mai matsakaicin shekaru.

Jihar Kaduna.
An Gano Wani Mutumi Tsirara Da Aka Kulle a Daki Tsawon Shekara 20 a Kaduna Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Mai magana da yawun jami'an duba garin wanda ya nemi a ɓoye bayanansa yace:

Kara karanta wannan

Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Mika Mulki, Buhari Ya jaddada

"Yau mun zo wannan gidan domin duba wasu kayan sha waɗanda aka saba aje wa a gida ba tare da tsaftar wuri ba lokacin da muka ci karo da Mutumin tsirara kulle a cikin daki."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun tarad da shi a yanayi mara kyau. Warin da ya rinka hitowa daga ɗakin lokacin da muka shiga gidan ba zai misaltu ba, daga baya muka ɓalla Kofar muka fito da shi."
"Yana abubuwa tamkar dabba, daga nan ne muka gano an tsare shi a ɗakin tsawon shekara 20. Komai a ɗakin yake yi, Fitsari, kashi da komai na rayuwa, anan ake ciyar da shi."

Wane mataki jami'an suka ɗauka?

Legit.ng Hausa ta gano cewa daga baya an gayyaci dakarun 'yan sanda na Caji Ofin ɗin Magajin Gari dake tsakiyar Kaduna, inda suka zo suka tafi da mutumin.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Wani Matashi Ya Naushi Abokinsa, Ya Faɗi Ya Mutu a Birnin Kano

Amma har zuwa yanzu da muke kawo muku wannan rahoton, babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar yan sanda reshen Kaduna.

A wani labarin kuma Tsautsayi Ya Ratsa Yayin da Wani Matashi Ya Naushi Abokinsa Ya fadi Ya Mutu a Kano

Dakarun 'yan sanda sun kama wani matashi ɗan shekara 18 a duniya, Saminu Bala, bisa zargin kashe abokinsa a jihar Kano.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, yace saɓani ne ya shiga tsakaninsu, Bala Ya daki Khalil.

Asali: Legit.ng

Online view pixel