Duk ‘Dan Da Yace Uwarsa Ba Za Ta Yi Bacci Ba: Uwa Ta Goya Diyarta A Bayan Mutum-Mutumi, Bidiyon Ya Kayatar

Duk ‘Dan Da Yace Uwarsa Ba Za Ta Yi Bacci Ba: Uwa Ta Goya Diyarta A Bayan Mutum-Mutumi, Bidiyon Ya Kayatar

  • Wata uwa ta kasa boye farin cikinta bayan ta samu sabuwar dabarar ajiye yarta cikin sauki
  • Uwar mai cike da hikima ta goya yarinyar a bayan wani butum-butumi sannan ta sa zanin atampa ta daure ta da kyau
  • Da ta ga cewa dabarar tata tayi aiki sosai, sai matar wacce ta cika da farin ciki ta mika godiyarta ga duk wanda ya kirkiri wannan dabarar

Wata yar Najeriya mai suna Kaotharomowumi a TikTok ta yi amfani da wata dabara kan diyarta kuma abun yayi aiki sosai.

Matar wacce ta gaji da fitinar diyar tata ta goya ta a bayan wani butum-butumi sannan tayi amfani da zanin atampa ta daureta da kyau.

Yarinya goye a bayan mutum-mutumi
Duk ‘Dan Da Yace Uwarsa Ba Za Ta Yi Bacci Ba: Uwa Ta Goya Diyarta A Bayan Mutum-mutumi, Bidiyon Ya Kayatar Hoto: @kaotharomowumi / TikTok
Asali: UGC

Ga mamakinta, sai ga yarinyar ta lafe a bayan mutum-mutumin harma ya kai ga tana murmusawa. Ta cika da farin ciki da ganin cewa dabarar tayi aiki.

Kara karanta wannan

Budurwa ta Bude Guruf a WhatsApp, Ta Tara Duk Samarinta Tare da Sanar Musu Zata yi Aure, Ta Fice ta Basu Wuri

Uwar da ta cika da farin ciki ta wallafa bidiyon a TikTok sannan tayi godiya ga mutum da farko da ya fara kirkiran wannan dabarar da tayi amfani dashi kan diyar tata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalamanta:

“Duk dan da yace uwarsa ba za ta yi bacci ba. Allah ya albarkaci wanda ya kawo wannan dabara.”

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@jennyfaar ta yi martani:

“Kafin nayi aure zan siya butum-butumi biyu na ajiye a gefe.”

@nelly_cute33 tace:

“Ki jira mahaifinta. Ko shakka babu zaki tafi gidan naki baban.”

@mummyades33 tace:

“Ke muguwa ce kuma yaron na kallonki.”

Range Rover Nake So: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Motar Wasan Yara Yayin da Ta Dame Shi Ya Siya Mata Mota

A wani labarin, wata matashiya ta wallafa dan takaitaccen bidiyo na abun da mahaifinta yayi a bikin zagayowar ranar haihuwar mahaifiyarta.

Kara karanta wannan

Da Sauran Aiki: Sanatar PDP Ta Gano Katuwar Matsala a Cikin Kasafin Kudin 2023

Kafin zuwan wannan rana, matar ta bukaci mijin nata da ya siya mata mota kirar Range Rover don raya wannan rana.

Mutumin ya gabatar mata da wata kyauta a kwali. Ya bude kwalin sannan ya nuna mata motar wasan yara. Mijin yace wannan ne Range Rover din da ya iya sama mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel