Da Sauran Aiki: Sanatar PDP Ta Gano Katuwar Matsala a Cikin Kasafin Kudin 2023

Da Sauran Aiki: Sanatar PDP Ta Gano Katuwar Matsala a Cikin Kasafin Kudin 2023

  • Sanata Better Apiafi tana ganin sai an yi gyare-gyare a kasafin kudin 2023 kafin a iya amfani da shi
  • ‘Yar majalisar ta koka a kan yawan satar danyen mai da ake yi da bashin da ake sake shirin karbowa
  • A majalisar wakilan tarayya, irinsu Hon. Nkeiruka Onyejeocha (APC, Abia) suna da wannan ra’ayi

Abuja - Sanata Better Apiafi mai wakiltar Ribas a majalisar dattawa tana ganin kundin kasafin kudin shekara mai zuwa na 2023 ba zai iya aiki ba.

Premium Times ta rahoto Better Apiafi tana cewa gwamnatin tarayya tayi kuskure a lissafi da alkaluman da tayi amfani da su cikin kasafin kudin badi.

Idan aka tafi a haka, Sanata Apiafi ta fadawa ‘yan jarida ba zai yiwu kasafin kudin ya yi aiki ba.

Da take jawabi, ‘yar majalisar mai wakiltar Ribas ta yamma ta koka a kan yadda gwamnati ta kyale barayi suna cigaba da satar arzikin kasar nan.

Za a cigaba da cin bashi

Sanatar jam’iyyar hamayyar ta kuma nuna cewa mafi yawan kudin da ake nema a 2023 za su fito ne ta hanyar neman bashi domin gibin da ake da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto, a ra’ayin ‘yar majalisar dole ne a kawo karshen satar danyen mai da tsageru suke yi a yankin Neja-Delta.

Majalisa
Buhari yana gabatar da kasafin kudin 2023 Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Better Apiafi ta bada shawara ga gwamnatin Muhammadu Buhari ta dage wajen neman kudin shiga, ta kuma yanke matsaya guda kan tallafin fetur.

Me gwamnati take yi, ta kyale ana satar dukiyar kasa – ta bar matsalar tsaro ya fi karfin gwamnati.

Me kuke yi? A maimakon a bar mu da abubuwa biyu a game da tallafin an fetur, me zai haka a fadada kudin shigan da kasar nan za ta iya samu?

Akwai bukatar ayi gyara

“Muna da babbar matsala. Ina tunani gwamnati tayi kuskure wajen alkaluman da tayi amfani da ita a kasafin nan. Suna bukatar su gyara kundin kasafin.
Kasafin ba za iyi aiki a haka ba. Ba zai yi aiki ba saboda dole sai mun karbo bashi. Kuma tallafin fetur zai ci kaso mai tsoka a wannan kasafin kudin.

Honarabul Nkeiruka Onyejeocha tana da wannan ra’ayi, tana ganin ba zai yiwu gwamnati ta cigaba da tafiya a tsarin da take kai a halin yanzu ba.

Jirgin Kaduna-Abuja zai cigaba da aiki

A baya an ji labari Ministan sufuri na tarayya, Mua’zu Jaji Sambo yace asusun gwamnati bai yi ciwo kafin a fito da fasinjojin jirgin da aka ceto ba.

A lokacin da ake farin cikin ceto ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su, Injiniya Sambo ya kuma ce jirgin kasan Abuja-Kaduna zai cigaba da yin aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel