Budurwa ta Bude Guruf a WhatsApp, Ta Tara Duk Samarinta Tare da Sanar Musu Zata yi Aure, Ta Fice ta Basu Wuri

Budurwa ta Bude Guruf a WhatsApp, Ta Tara Duk Samarinta Tare da Sanar Musu Zata yi Aure, Ta Fice ta Basu Wuri

  • Matashiyar budurwa ta bude guruf din WhatsApp inda ta tattaro dukkan samarin da ta taba yi a rayuwarta
  • Sai dai niyyarta tafi zama abun mamaki saboda ta sanar da su ne cewa kada su dake kulata don zata yi aure
  • Prince Mudi, daya daga cikin samarin da tayi wannan shegantakar ya bayyana labarin yadda lamarin ya faru a Twitter

Wani matashi ‘dan Najeriya ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi cike da abun mamaki.

Matashin mai suna Prince Mudi yace budurwar ta fara da bude guruf din WhatsApp ne sannan ta saka shi a ciki.

Budurwa
Budurwa ta Bude Guruf a WhatsApp, Ta Tara Duk Samarinta Tare da Sanar Musu Zata yi Aure, Ta Fice ta Basu Wuri. Hoto daga @princemudi
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan kirkirar guruf in da tayi, sai ta sanar da ranar aurenta sannan ta fice ta basu wuri.

Kara karanta wannan

Duk ‘Dan Da Yace Uwarsa Ba Za Ta Yi Bacci Ba: Uwa Ta Goya Diyarta A Bayan Mutum-mutumi, Bidiyon Ya Kayatar

Sai dai guruf din da ta bude ta saka dukkan mazan da ta taba soyayya dasu saboda tana son basu sanarwa mai muhimmanci.

Abu na gaba

Niyyarta shi ne ta rabu da dukkansu a lokaci daya sannan ta fara sabuwar rayuwarta da sabon saurayin da ta samu.

Aure zan yi

Prince Mudi yace budurwar ta sanar da cewa aure zata yi a mako mai zuwa sannan ta fice daga guruf din tare da bari sue su jajantawa juna abinda ta sanar musu.

A wallafar Twitter, Prince Mudi yace:

“A 2017 na taba soyayya da wata budurwa na tsawon shekara daya. A wani dare kawai ta sanya ni a wani guruf na WhatsApp kuma tace “dukkanku kune mazan da bana so kuma ya zo karshe saboda aure zan yi karshen mai mai zuwa.”
“A take ta fice daga guruf din kuma ta bar mu muna sake sanin juna.”

‘Yan Twitter sun yi Martani

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Fusata, Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ya Ki Zuwa Daukarta A Filin Jirgin Sama

@ohlynxx93 yace:

“Abun takaicin shine diyarta ce zata sha wahalar laifin da mahaifiyarta ta tafka. Tsurar gaskiya.”

@Chukwuemekazee yayi tsokaci da:

“Babu wata wahalar da diyarta zata sha.”

@PeccaviConsults yace:

“Kawai dukkanku ku dinka kaya, ku halarci auren a matsayin kawayen Amarya.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel