Budurwa Ta Fusata, Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ya Ki Zuwa Daukarta A Filin Jirgin Sama

Budurwa Ta Fusata, Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ya Ki Zuwa Daukarta A Filin Jirgin Sama

  • Wata matashiyar budurwa ta datse igiyar soyayyarsu da saurayinta bayan ya ki zuwa ya dauke ta a filin jirgin sama
  • Matashiyar mai suna Masango Sisanda ta je shafin Twitter don bayar da labarin abun da ya faru tsakaninsu kuma nan take ta haddasa cece-kuce
  • Yayin da wasu suka ce hakan bai isa dalilin rabuwarsu ba, wasu na ganin abun da budurwar tayi shine daidai

Wata matashiyar budurwa ta rabu da saurayinta saboda ya ki zuwa ya dauketa a filin jirgin sama a lokacin da ta dawo daga tafiya.

A cewar matar mai suna Masango Sisanda, saurayin nata ya bata uzurin da sam bata gamsu da shi ba.

Budurwa da jirgin sama
Budurwa Ta Fusata, Ta Rabu Da Saurayinta Saboda Ya Ki Zuwa Daukarta A Filin Jirgin Sama Hoto: Twitter/@MasangoSisanda and Aaron Foster/Getty Images.
Asali: UGC

Mesango ta je shafin Twitter don bayyana yadda ta kira saurayinta amma yace shi ayyuka sun sha kansa kuma ba zai samu zuwa daukarta a filin jirgin sama ba.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Saci Sabon Jariri A Asibitin ATBUTH Dake Bauchi

Wasu mutane sun caccaketa kan datse soyayyarsu da tayi, amma ta kare kanta, tana mai cewa dabi’ar saurayin nata ne cutar da zuciyarta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mesango ta dawo ne daga jana’zar kakanta

Mesango ta kuma bayyana cewa bata samu sabon saurayi ba. Kalamanta:

“Da farko, bani da sabon saurayi bani da kowa yanzu. Abu na biyu, ban rabu dashi saboda wani lamari na takura ba.
“Na rabu dashi ne saboda na gaji da yadda yake azabtar da zuciyata da juyata a koda yaushe. Ya faru nbe saboda abun ya bata mun rai har ta kai nace kowa ya bi hanyarsa.”

Mesango ta ce ta dawo ne daga jana’izar kakanta lokacin da ta kira saurayin nata kuma yaki lallashinta a lokacin da take alhini.

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@rereayodele ta ce:

Kara karanta wannan

Cosmas Maduka: Attajirin Da Bai Taɓa Zuwa Makaranta Ba, Ko Talabijin Bai Da Shi

"Shin sabon saurayinki ya san cewa kwanan nan shima zaki maye gurbinsa da wani saboda kina canja maza ne kan dan abu da bai taka kara ya karya ba."

@_beeebii gta ce:

"Kowa fushi yake yi kwanan nan...dan karamin kuskure ka fita daga layi."

@monomyth_ivxx ta ce:

"Dauka daya daga filin jirgin zama ya tayar da soyayyar sama."

Budurwa Ta Yi Murabus Daga Wajen Aikinta A Amurka, Ta Siyar Da Kayayyakinta, Ta Koma Ghana Saboda Namiji

A wani labarin, wata matashiya mai suna Abbey ta yi fice a TikTok bayan ta yi murabus daga aikinta a kasar Amurka sannan ta koma Ghana da zama.

Abbey ta kuma siyar da mota da kayan gidanra kafin tayi balaguro.

A cewar Abbey, ta yi kaura ne saboda masoyinta na Ghana kuma ba za ta iya ci gaba da zama nesa dashi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel