Budurwa Ta Yi Murabus Daga Wajen Aikinta A Amurka, Ta Siyar Da Kayayyakinta, Ta Koma Ghana Saboda Namiji

Budurwa Ta Yi Murabus Daga Wajen Aikinta A Amurka, Ta Siyar Da Kayayyakinta, Ta Koma Ghana Saboda Namiji

  • Wata kyakkyawar budurwa ta haddasa cece-kuce a TikTok bayan ta bar kasar Amurka inda ta koma Ghana da zama domin rayuwa tare da masoyinta
  • Wani bincike a kan shafinta na TikTok ya nuna cewa tayi aure ne yan watanni da suka gabata kuma ba za ta iya ci gaba da zama nesa da mijinta ba
  • Budurwar mai suna Abbey ta auri dan Ghana sannan ta ce zuciyarta na chan kasar wanda shine dalilinta na dawowa

Wata matashiya mai suna Abbey ta yi fice a TikTok bayan ta yi murabus daga aikinta a kasar Amurka sannan ta koma Ghana da zama.

Abbey ta kuma siyar da mota da kayan gidanra kafin tayi balaguro.

Masoya
Budurwa Ta Yi Murabus Daga Wajen Aikinta A Amurka, Ta Siyar Da Kayayyakinta, Ta Koma Ghana Saboda Namiji Hoto: TikTok/@_theblessedhalls.
Asali: UGC

A cewar Abbey, ta yi kaura ne saboda masoyinta na Ghana kuma ba za ta iya ci gaba da zama nesa dashi ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Hirar Da Aka Yi Da Matar Da Ke Auren Maza 2, Ta Ce A Gado Ɗaya Suke Kwana Kuma Suna Zaman Lafiya

Wani bincike a shafinta na TikTok ya nuna ‘daga USA zuwa Ghana’ yana nuna cewa lallai ta sauya zuciyarta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika, wasu yan bidiyoyi a shafinta na TikTok sun nuna cewa kwanan nan ta auri hadadden saurayi dan Ghana. Ta koma US bayan nan.

Don haka ta sake komawa don kasancewa tare da masoyinta a sabon gidanta, wanda a wurinta wannan shine yafi komai muhimmanci a yanzu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

@Pretty Gifty ta ce:

“Hmmm ni kuma ina son barin Ghana zuwa Amurka. Rayuwar nan ba daidai bane.”

@Stella Shanelly ta yi martani:

“Barka da dawowa gida.”

@Angelica Pemberton Nsiah tace:

“Kwarai, ina ma ace zan iya bin ki, kawai ina so na kasance a Ghana tare da mijina.”

@nanakwame10k ta yi martani:

Kara karanta wannan

Wannan Shekarar Tazo da Albarka: Budurwar Da Tayi Wata 5 Tana Kwana a Kasa Ta Siya Sabon Gado Dal

“Ghana ne wuri mafi dadin zama idan kana da kudi.”

Range Rover Nake So: Miji Ya Gwangwaje Matarsa Da Motar Wasan Yara Yayin da Ta Dame Shi Ya Siya Mata Mota

A wani labarin, wata matashiya ta wallafa dan takaitaccen bidiyo na abun da mahaifinta yayi a bikin zagayowar ranar haihuwar mahaifiyarta.

Kafin zuwan wannan rana, matar ta bukaci mijin nata da ya siya mata mota kirar Range Rover don raya wannan rana.

Mutumin ya gabatar mata da wata kyauta a kwali. Ya bude kwalin sannan ya nuna mata motar wasan yara. Mijin yace wannan ne Range Rover din da ya iya sama mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel