Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

  • Ruftawar wani gini mai bene ɗaya ya yi sanadin rasuwar wani yaya da kaninsa a unguwar Kofar Mata a Kano
  • Saminu Abdullahi, mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na Jihar Kano ya sanar da hakan a ranar Asabar
  • Abdullahi ya ce sun samu kiran neman dauki misalin ƙarfe 10.50 na dare kuma suka tura tawaga ta cire biyu ba su numfashi daya kuma ya jikkata

Jihar Kano - Wani gini mai hawa ɗaya ya rufta a ranar Juma'a, ya yi sanadin rasuwar yaya da kani masu shekaru 15 da 11.

Babban yayansu mai shekaru 17, shi an yi nasarar ceto shi da ransa, Premium Times ta rahoto.

Taswirar Kano
Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3, Biyu Cikinsu Sun Mutu. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana na Jihar Kano, Saminu Abdullahi, a ranar Asabar ya ce gidan da abin ya faru yana unguwar Kofar Mata, Hauren Gadagi a Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Kalamansa:

"Mun samu kiran neman dauki misalin ƙarfe 10.50 na dare daga wani Jamilu Salisu Zango cewa wani gini mai fadin kafa 50 * 40 da ake zaune a cikinsa ya rufta daga sama zuwa kasa.
"Mun aika da tawagar mu zuwa wurin suka fito da yan gidan dayan daga baraguzan ginin. Biyu cikin su ba su numfashi."

Mr Abdullahi ya kara da cewa an garzaya da wadanda abin ya faru da su zuwa Asibitin Murtala Muhammad don likitoci su duba su idan aka tabbatar biyu cikinsu sun rasu.

An mika wa yan sandan Kofar Wambai gawarwakin, yayin da an fara bincike kan afkuwar lamarin in ji shi.

An Ceto Mutum 3 Daga Ginin Da Ya Rufta A Kasuwar Kano, Akwai Saura Da Aka Kasa Fito Da Su

A wani rahoto mai kama da wannan, wani gini da ake kan aikinsa ya rushe a daya daga cikin kasuwannin wayoyin salula wato GSM a Kano.

Kara karanta wannan

An Kama Fursunan Da Ya Tsere Daga Kuje Ya Yada Zango A Kano

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ginin yana Beirut road ne, wani layi da mutane kan yawan hada-hada.

Ana fargabar mutane da dama sun makale a ginin da ya rufta duk da cewa a yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel