Gaskiya Ta Fito: 'Yadda Muka Shawo Kan Yan Ta'adda Suka Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja'

Gaskiya Ta Fito: 'Yadda Muka Shawo Kan Yan Ta'adda Suka Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja'

  • Farfesa Usman Yusuf, ya ce sun shafe tsawon watanni shida suna kokarin ganin an saki fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja ba tare da an biya sisi ba
  • Sakataren kwamitin shugaban ma’aikatan tsaro ya ce sun fadama yan ta'addan addini bai yarda da garkuwa da mata masu juna biyu da yara ba
  • Ya kuma tabbatar da cewar yan Boko Haram ne suka yi garkuwa da fasinjojin ba yan Ansaru ba

Sakataren kwamitin mutum bakwai na shugaban ma’aikatan tsaro, Farfesa Usman Yusuf, ya magantu kan al’amarin sakin fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Farfesa Yusuf yace sun shafe tsawon watanni shida suna aiki ta karkashin kasa domin tabbatar da ganin cewa an saki fasinjojin ba tare da an biya fansa ba, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yadda Hadimin Gumi ya Dinga Tarwatsa Kokarin FG na Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa, Jami’i

Hakan ya kasance ne yayin da yace kwamitinsu bai karfafa biyan yan ta’addan kudin fansa ba.

Jirgin kasa
Gaskiya Ta Fito: 'Yadda Muka Shawo Kan Yan Ta'adda Suka Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja' Hoto: @ChibuikeAmaechi
Asali: Facebook

Da yake zantawa da muryar Amurka, Farfesa Yusuf ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Bamu ba yan ta’addan ko sisin kwabo don su sako mutum 23 da suka tsare ba.”

Ya ce tun a ranar 29 ga watan Maris 2022 da kwamitin ya fara aiki sun fadawa yan ta’addan cewa ba daidai bane yin garkuwa da mata masu ciki da kananan yara.

Ya kara da cewa:

“Mun fada masu babu inda addinin Musulunci ya karfafa haka. Muna ta rokonsu da su sake duba matsayinsu sannan su saki mutanen da suka yi garkuwa da su.”

Sai dai kuma, ya ce:

“Muna tattaunawa kwatsam sai muka fara jin yan uwa sun shigo cikin lamarin suna neman a saki masoyansu da kuma biyan kudin fansar.

Kara karanta wannan

Sojinmu Gwaraza ne, Babu Aikin da Ba Zasu Iya ba: Buhari Yana Murnar Dawowar Fasinjojin Jirgin Kasa

“Don gujema duk wani shakku, bamu karfafa biyan kudin fansar ba tun daga farko. Kuma a lokacin da muka gano an saki kowa sauran mutum 23. Sai muka shiga damuwa. Mun yi tunanin sauran mutanen ba lallai ne suna da kudin ba. Shakka babu za a barsu su rube.
“Daga cikin mutum 23 da ke tsare akwai wata yarinya yar shekara biyu. A lokacin da aka yi garkuwa da ita bata kai shekaru biyu ba. Mun fada masu ba daidai bane yaki da gwamnati.
“Mun shiga daji don ganawa dasu yan Boko Haram. Muna ta ganawa da wasu mutanen, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin Fulani, jami’an sojin sama, kasa da na ruwa.
“Rundunar soji sun taka muhimmiyar rawar gani. Ba don gudunmawar shugaban ma’akatan tsaro, Janar Irabor ba, da bamu samu damar shiga jeji ba. Kuma da duk hakan bai yiwu ba idan ba daban samun cikakken goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.”

Kara karanta wannan

Hotunan Sauran Fasinjoji 23 na Jirgin Kasan Abj-Kd da Suka yi Kwana 192 Hannun ‘Yan Ta’adda

A cewarsa, mutanen da suka yi garkuwa da mutum 63 ba yan Ansaru bane, yan Boko Haram ne.

Ya kuma ce kwamitin ya tattauna sosai da yan ta’addan yana mai cewa:

“Ba mutum-mutumi bane su, mutane ne. ba daga sama suka fado ba.
“Ina ganin ya kamata a ci gaba da tattaunawar don tabbatar da ganin zaman lafiya ya dawo kasarmu.
“Ya kamata mu ci gaba. Hakan zai yiwa daga abun da na gani. Kun san na bi Shiekh Gumi zuwa jihohi takwas inda ya tattauna da yan ta’adda. Mun sha fadin cewa ya kamata a zauna da su ayi sulhu.
“Babban abun shine kwamitinmu ya bude kafar tattaunawa da su na hakika. Zan so fadin cewa ya kamaya a bari ya zo karshe.”

Kan barazanar da kwamandan Boko Haram yayi na auren Azurfa Lois John mai shekaru 21, sakataren kwamitin yace ba gaskiya bane.

“Hatta yan kwanaki kafin sakinsu, kwamandan ya jadadda cewa bai taba fadin haka ba. Hatta lokacin da muka tattauna da ita, ta ce ba gaskiya bane. Kwamandan bai taba tunkararta ba."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ‘Yan Ta’adda Sun Sako Sauran Fasinjoji 23 na Harin Jirgin Kasan Abj-Kd

‘Yan Ta’adda Sun Sako Sauran Fasinjoji 23 na Harin Jirgin Kasan Abj-Kd

A baya mun ji cewa ‘Yan ta’adda da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sako ragowar fasinjoji 23 da suka yi garkuwa da su.

Sakataren kwamitin shugaban ma’aikatan tsaro, Usman Yusuf ne ya tabbatar da hakan kamar yadda Channels Tv ta rahoto.

Yusuf yace an sako fasinjojin da suka kwashe watanni shida hannun miyagun ‘yan bindigan a ranar Laraba wurin karfe 4 na yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel