Sojinmu Gwaraza ne, Babu Aikin da Ba Zasu Iya ba: Buhari Yana Murnar Dawowar Fasinjojin Jirgin Kasa

Sojinmu Gwaraza ne, Babu Aikin da Ba Zasu Iya ba: Buhari Yana Murnar Dawowar Fasinjojin Jirgin Kasa

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana murnarsa game da dawowar fasinjoji 23 da suka yi kwanaki 191 hannun Boko Haram
  • Buhari ya yabawa dakarun sojin Najeriya kan kokarinsu inda yace gwarzaye ne zasu iya kowanne irin aiki
  • Har ila yau, shugaban ya taya iyalan fasinjojin murnar yadda ‘yan uwansu suka dawo gida a raye ba tare da na rasa ko mutum daya ba

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya bayyana farin cikinsa kan sakin fasinjoji 23 na jirgin kasa da suka dade a hannun ‘yan ta’adda.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Laraba ta wallafar da yayi a shafukansa na soshiyal midiya, jaridar TheCable ta rahoto.

Abuja
Sojinmu Gwaraza ne, Babu Aikin da Ba Zasu Iya ba: Buhari Yana Murnar Dawowar Fasinjojin Jirgin Kasa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Hotunan Sauran Fasinjoji 23 na Jirgin Kasan Abj-Kd da Suka yi Kwana 192 Hannun ‘Yan Ta’adda

A ranar Laraba aka rahoto yadda fasinjoji 23 na farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suka shaki iskar ‘yanci.

Wannan ‘yancin ya biyo bayan watanni shida da suka kwashe hannun maharan.

Kamar yadda gwamnatin tarayya ta bayyana, kwamitin fadar shugaba kasa na mutum bakwai karkashin shugabancin Janar Lucky Irabor, shugaban ma’aikatan tsaro, suka ceto fasinjojin.

A yayin martani a wallafar da yayi, Buhari yace kasar tana mika godiya ga sojoji da sauran jami’an tsaro da na sirri kan nasara da suka samu a aikin.

“Cike da dumbin farin ciki nake maraba da sakin sauran fasinjoji 23 da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su. Kamar dukkan kasar, ina farin ciki da wannan labarin kuma muna godiya ga sojoji da sauran hukumomin tsaro.”

- Yace.

“Dakarun sojin kasar mu da sauran hukumomin tsaro gwarzaye ne kamar kowanne. Samun goyon baya da kwarin guiwa kamar yadda muka saba yi, babu wani aiki da zai gagaresu. Ina yaba musu kan wannan sakamakon.

Kara karanta wannan

A Shekaru 3 a Ofis, Mun Kammala Ayyuka Fiye da 2000 a Ma’ikatarmu – Isa Pantami

“Ina taya iyalan wadanda aka sako murna kan yadda suka dawo gida a raye.
“Na yi gamsasshen bayani ga jami’an tsaron mu kan yadda suka dage wurin yaki da ta’addanci dole ya cigaba domin ganin karshen ‘yan bindiga da garkuwa da mutane a fadin kasar nan.
“Dole ne mu cigaba da aiki wurin kare dukkan fadin kasarmu.”

- Shugaban kasar yace.

Da Duminsa: ‘Yan Ta’adda Sun Sako Sauran Fasinjoji 23 na Harin Jirgin Kasan Abj-Kd

A wani labari na daban, ’yan ta’adda da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sako ragowar fasinjoji 23 da suka yi garkuwa da su.

Sakataren kwamitin shugaban ma’aikatan tsaro, Usman Yusuf ne ya tabbatar da hakan kamar yadda Channels Tv ta rahoto.

Yusuf yace an sako fasinjojin da suka kwashe watanni shida hannun miyagun ‘yan bindigan a ranar Laraba wurin karfe 4 na yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel