A Karon Farko, An Nada Mace Matsayin Shugaban Babban Jami'a A Najeriya

A Karon Farko, An Nada Mace Matsayin Shugaban Babban Jami'a A Najeriya

  • Shugaban jami'ar Legas mai barin gado, Farfesa Toyin Ogundipe, zai mika jagoranci ga sabuwar VC, Farfesa Folasade Ogunsola, nan bada dadewa ba
  • A ranar 7 ga watan Oktoban 2022, an sanar da nadin Farfesa Ogunsola a matsayin mace na farko da za ta jagoranci jami'ar
  • Ogunsola, farfesa a bangaren nazarin kananan hallittu wato Microbiology, ya ce ga marigayi Farfesa Akin Mabogunje

Jihar Legas - An nada Farfesa Folasade Ogunsola a matsayin mace ta farko da ta fara zama shugaban jami'ar Legas (UNILAG), Daily Trust ta rahoto.

Ogunsola ta yi nasara ne cikin mutane bakwai da aka tantance sunayensu don nadin mukamin.

Folashade
A Karon Farko, An Nada Mace Matsayin Shugaban Babban Jami'ar Legas. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Atiku Abubakar a PDP Ya Samu Mukami a Kwamitin Neman Zabensa

Wadanda suka nemi mukamin shugabancin jami'ar Legas

Daga cikin sauran mutanen da aka tantance akwai Akinyeye na Tsangayar Tarihi; Mathew Ilori da Adeyinka Adekunle na Sashin Nazirin Kananan Halitu da Tsirai; Imran Smith, Tsangayar Koyar da aikin shari'a; Timothy Mubi na Tsangayar Nazarin Gidaje Da Filaye da Ayo Olowe na Tsangayar Bangaren Kudi sai ita Folashade Ogunsola Na Kwallejin Likitanci.

Takaitaccen tarihin Farfesa Ogunsola

An haife Ogunsola a shekarar 1958, kuma Farfesa ce a bangaren nazarin kananan hallitu masu alaka da kiwon lafiya kuma kwararriya a sashin nazarin cuttuka masu yaduw a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Legas.

Ta kware a bangaren kiyaye kamuwa da cututtuka musamman Kanjamau wato HIV/AIDS. Ogunsola ta taba rike shugaba a Kwallejin Koyar da Likitanci. Ta kuma taba rike mukamin mataimakiyar shugaban jami'ar daga 2017 zuwa 2021.

Majalisar zartarwa na jami'ar ta zabe ta a matsayin shugaban jami'ar Legas na rikon kwarya a ranar 24 ga watan Agustan shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari Ya Gana Da Sauran Fasinjojin Jirgin Kasa 23 Da Aka Sako Jiya

A Ci Gaba da Yi: Dalibin Jami’a Ya Kama Sana’a, Ya Ce ASUU Su Tabbata Suna Yaji Kawai

Abdulhadi Dankama ya samu shiga sashen ilmin lissafi a jami'ar Bayero ta jihar Kano domin yin digirinsa na farko.

Ya kamata Dankama ya kammala digirinsa a yanzu idan da yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta fara ba kan rashin jituwa da gwamnatin tarayya bata shafe shi ba.

Za ku yi tunanin Dankama wanda a yanzu yana aji 3 zai kosa ya koma makaranta domin ya gaggauta kammala karatunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel