Shugaba Buhari Ya Gana Da Sauran Fasinjojin Jirgin Kasa 23 Da Aka Sako Jiya

Shugaba Buhari Ya Gana Da Sauran Fasinjojin Jirgin Kasa 23 Da Aka Sako Jiya

Shugaba Buhari Ya Gana da Fasinjojin Jirgin Kasa 23 Da Aka Yi Garkuwa Da Su...

A ranar Alhamis din ne shugaba Muhammadu Buhari ya gana da tsararrun fasinjojin jirgin kasa 23 wadanda aka sace a a kan hanyar Abuja-Kaduna a asibitin Soji (NDA) da ke Kaduna.

Wannan ziyara ce ta gaggawa da shugaban ya shirya domin ganin wadanda suka gamu da wannan ibtila'i bayan kaddamar da jami'an soja da suka kammala karbar horo karo na 69 a Afaka a jihar Kaduna.

Bayan wannan biki ne kuma, shugaban kafin komawa Abuja ya biya ta wannan asibiti domin duba lafiyarsu tare da yaba wa rundunar sojin kasar nan bisa namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da sakin fasinjojin da Boko Haram suka tsare.

Kara karanta wannan

Sojinmu Gwaraza ne, Babu Aikin da Ba Zasu Iya ba: Buhari Yana Murnar Dawowar Fasinjojin Jirgin Kasa

Haka su ma manyan mambobin rundunar soja na ofishin babban hafsan sojan kasar nan, a bisa jagorancin manjo-janar Usman Abdulkadir mai ritaya sun kasance a asibitin.

Sauran sun hada da: Manjo-Janar Adamu Jalingo (mai ritaya) da birgediya-Janar Abubakar Saad (mai ritaya) da dakta Murtala Ahmed Rufai da Ibrahim Abdulllahi, Ambasada Ahmed Magaji da farfesa Yusuf Usman a matsayin magatakarda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yan kwanakin da suka wuce ne shugaban hafsan sojin kasar na LEO Irabor ya kafa tare da gabatar da su a matsayin kwamiti ga shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel