Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudi a Yau, Tsaro ya Tsananta a Farfajiyar Majalisa

Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudi a Yau, Tsaro ya Tsananta a Farfajiyar Majalisa

  • Tsaro ya tsananta a ginin majalisar tarayyar Najeriya yayin da Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2023 a yau Juma’a
  • Kamar yadda aka gano, wannan ne karo na karshe da shugaban kasan zai gabatar da kasafin inda zai mika na N19.6t
  • Za a kayyade masu shiga zauren majalisar tun daga kan manema labarai, jami’an tsaro da ma’aikata don gujewa cunkoso

An tsananta tsaro a majalisar tarayyan Najeriya kafin zuwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin gabatar da kasafin kudin 2023 a yau Juma’a.

Shugaban Kasan zai gabatar da kasafin N19.76 tiriliyan ga zauren gamayya na majalisar dattawa da wakilai da karfe 10 na safe.

Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2023
Buhari zai Gabatar da Kasafin Kudi a Yau, Tsaro ya Tsananta a Farfajiyar Majalisa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wannan ne karo na karshe da shugaban kasan zai gabatar da kasafin kudi gaban majalisar saboda wa’adin mulkinsa zai kare a watan Mayun 2023, Daily Trust ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

Biliyoyin da Shugabanni Suka Wawure Daga Najeriya Suna Dankare a Turai, Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa, majalisar dattawa da na wakilai ana gyara su, lamarin da yasa dukkan ‘yan majalisar suka sauya wurin zama.

Zauren majalisar wucin-gadin mai lambar daki 0.28 yana da mazaunai 118. An fadada shi zuwa daki na 231 da kuma wurin zama 236.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, yace an kammala duk shirin da za a yi domin bai wa ‘yan majalisar wurin zama tare da shugaban kasan da tawagarsa.

Za a kayyade yawan masu shiga majalisar saboda za a yi tantancewa ta musamman ga manema labarai, jami’an tsaro da ma’aikatan majalisar da zasu yi aiki yayin gabatarwan.

An gano cewa, ma’aikatan da basu da hannu cikin tsarin an bukaci su huta a gida yayin da bankuna da sauran kasuwancin dake gudana a wurin aka bukaci su rufe shagunansu.

Kara karanta wannan

A karon farko: Diyar Atiku ta fito a jerin matasan da za su yi yawon kamfen din PDP

Shugaban Buhari Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2023 Gaban Majalisa

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudi N19.76 tiriliyan na shekarar 2023 ga majalisar tarayyar kasar nan a ranar Juma’a.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a zaman majalisar na ranar Talata, yace shugaban kasar zai yi wannan gabatarwan da karfe 10 na safe a zauren majalisar wakilai na wucin-gadi

Asali: Legit.ng

Online view pixel