'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Shugaban Al'umma a Jihar Filato

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Shugaban Al'umma a Jihar Filato

  • Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Sanannen jagoran al'umma, Gashon Leks, a yankin ƙaramar hukumar Mangu, jihar Filato
  • Mazauna ƙauyen Daika, inda lamarin ya faru sun nuna damuwarsu saboda mutumin yana fama da rashin lafiya
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, Alabo Alfred, yace labarin garkuwa da Mista Leks bai iso ofishinsa ba

Plateau - Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani fitaccen jagoran al'umma, Gashon Leks, wanda ya kasance babban yaya ga jami'in hukumar Soja da ya yi ritaya a yankin, Air Vice Marshal Leks, a jihar Filato.

Wasu mazauna ƙauyen Daika da suka zanta da jaridar Punch ranar Laraba a Jos, sun koka game da sace shugabansu, sun ce tuni suka sanar da jami'an tsaro lamarin mara daɗi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Halaka Wani Babban Malamin Musulunci a Arewacin Najeriya

Harin yan bindiga a Filato.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Shugaban Al'umma a Jihar Filato Hoto: punchng
Asali: Twitter

Ɗaya daga cikin mazauna yankin, Mathew Chai, yace ɗan uwan babban jami'ain sojin na zaune a gidansa da ke Daika lokacin da maharan suka shiga da misalin ƙarfe 10:00 na daren Litinin.

A cewarsa bayan sun shiga ƙauyen da dare, maharan sun yi awon gaba da Mutumin zuwa maɓoyarsu da ba'a sani ba yayin da suka tsorata mazauna da harbin bindiga.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mista Chai yace:

"Bamu sake jin duriyar mutumin ba tun lokacin da 'yan bindigan suka tasa shi. Sunansa Mr. Gashon Leks, mutumin manomi ne kuma yana wasu kasuwancin, sannan ya kasance yayan Air Vice Marshal Leks."
"Lamarin ya faru ranar Litinin da daddare da misalin ƙarfe 10:00. Maharan sun zo da yawa saboda rarraba kansu suka yi a sassan ƙauyen sanna suka buɗe wuta daga bisani suka tasa abin harinsu."
"Tun ranar Litinin babu wanda ya san inda mutumin yake, sai yau Laraba masu garkuwan suka bari ya yi magana da iyalansa kuma a iya fahimtata ba su nemi fansa ba har yanzu."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Kazamin Hari, Sun Halaka Bayin Allah Sama da 10 a Jihar Arewa

Chai ya ƙara da cewa mutane sun shiga tashin hankali saboda mutumin yana fama da rashin lafiya kafin sace shi kuma mutane sun damu sosai, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Shin hukumar 'yan sanda ta san da lamarin?

Yayin da aka nemi jin ta bakinsa, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Alabo Alfred, yace hukumarsu ba ta da masaniya kan lamarin.

"Bani da masaniya kan sace ɗan uwan jami'in soji mai ritaya a ƙaramar hukumar Mangu. Rahoton faruwar lamarin bai kai ga zuwa Ofishina ba, amma zan kira DPO na yankin sannan na dawo gare ku."

A wani labarin kuma Bello Turji Da Wani Hatsabibin Dan Bindiga Sun Kaure da Yaƙi a Zamfara

Wasu rahotanni sun nuna cewa tsagin Bello Turji ya kaure da azababben faɗa da ɓangaren wani shugaban 'yan ta'adda, Ɗan Bokolo.

Wata majiya tace tawagar yan ta'addan biyu sun barke da yaƙi ne baya kai wasu hare-hare kauyuka a Shinkafi.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: Wani Gwamnan Arewa Ya Fusata, Ya Dakatar da Biyan Malaman Jami'ar Jiharsa Albashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel