Mutane '30' da Suka Gudo Wa Harin Yan Bindiga a Zamfara Sun Nutse a Ruwa

Mutane '30' da Suka Gudo Wa Harin Yan Bindiga a Zamfara Sun Nutse a Ruwa

  • Wasu mutane mata da kananan yara da suka yi kokarin tserewa harin yan bindiga sun nutse a ruwa a Zamfara
  • Haɗarin ya auku ne bayan mutanen sun gudo daga kauyen Birnin Waje, karamar hukumar Bukkuyum, sa'ilin da yan bindiga suka farmake su
  • Bayanai sun nuna cewa har yanzu ba'a gama tsamo gawarwakin mutanen ba saboda fargabar zuwan yan ta'addan

Zamfara - Aƙalla mutane 30 da suka gudo daga harin ta'addancin yan bindiga a ƙauyen Birnin Waje, ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara sun rasa rayukansu sakamakon nutsewar Kwale-Kwalen da suke ciki.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilin Daily Trust cewa Kwale-Kwale biyu da aka cika da mutane fiye da ƙima sun nutse ranar Laraba da daddare.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wata Fashewa Ta Halaka Rayukan Mutane, Ta Yi Mummunar Ɓarna a Wata Jiha

A cewarsu jiragen biyu sun nutse ne yayin da suka yi yunkurin tsallake wani Tafki da nufin tsere wa harin da 'yan ta'adda suka kai ƙauyen su.

Haɗari ya rutsa da mazauna a Zamfara.
Mutane '30' da Suka Gudo Wa Harin Yan Bindiga a Zamfara Sun Nutse a Ruwa Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A 'yan makonnin nan, 'yan bindigan Daji sun zafafa kai hare-haren ta'addanci a ƙauyukan dake ƙaramar hukumar Bukkuyum. Kwana 13 da suka gabata mahara suka kashe Masallata 15 a Masallacin Ruwan Jema dake yankin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda lamarin ya faru

A harin ranar Laraban nan, mazauna sun ce yan ta'adda sun farmaki ƙauyen Birnin Waje, suka buɗe wa mutane wuta. Harbin maharan ya sa mutane suka fara kokawar neman tsira.

An ce mutane da yawa suka hau Kwale-kwalen guda biyu domin tsallake tafkin zuwa Zauma, garin da suke ganin ya fi zaman lafiya mai nisan kilomita biyu a yammacin garin Bukkuyum.

Sakamakon haka jiragen ruwan suka yi nauyi fiye da ƙima domin babu wanda ya yarda a barshi a wurin. Duk da gargaɗin da matuƙa Kwale-Kwalen suka wa mutanen don su ragu, ba wanda ya yarda kuma a haka suka tafi.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Fitaccen Jagoran Al'umma a Jihar Arewa

Wani mazaunin yankin, Babangida Bukkuyum, yace:

"Ana haka 'yan bindigan suka biyo mutanen da suka tsere har Tafkin suka rinka harbinsu. Suna tsakiyar ruwa, matuƙa Kwale--kwalen da suka ga ba zasu iya jure wa harbin ba suka faɗa cikin ruwa."
"Duk da haka wasu mutane sun tsira bayan sun faɗa suka yi ninƙaya zuwa gabar tafkin. 'Ya'yan ƙanwata uku na cikin waɗanda haɗarin ya shafa. Har yanzun ana fargabar maharan na kewayen yankin, hakan ya hana tsamo mutanen."

Da aka nemi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ba'a same shi ba domin jin ta bakinsu har zuwa yanzu da muke haɗa rahoton.

A wani labarin kuma kun ji cewa Bello Turji Da Wani Hatsabibin Dan Bindiga Sun Kaure da Yaƙi a Zamfara

Wasu rahotanni sun nuna cewa tsagin Bello Turji ya kaure da azababben faɗa da ɓangaren wani shugaban 'yan ta'adda, Ɗan Bokolo.

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari Chibok, Sun Sheke Rai 3

Wata majiya tace tawagar yan ta'addan biyu sun barke da yaƙi ne baya kai wasu hare-hare kauyuka a Shinkafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel