Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, Bola Tinubu, zai dawo gida Najeriya a ranar Juma'a ko kafin ranar
  • Majiyoyi sun bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Lagas zai halarci wani babban taro mai muhimmanci a ranar Juma'a a Abuja
  • Tinubu dai ya shafe tsawon wasu kwanaki a kasar Ingila inda hadimansa suka ce ya je shirya manufofinsa ne

Abuja - Ana sanya ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai dawo kasar a ranar Juma’a ko kafin ranar, jaridar TheCable ta rahoto.

Dan takarar jam’iyyar mai mulki ya shafe tsawon wasu yan kwanaki baya a kasar nan. Lamarin ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya inda ake ta cigiyar ina Tinubu ya shiga.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

Hakan ya samo asali ne bayan rashin ganin tsohon gwamnan na jihar Lagas a wajen kulla yarjejeniyar zaman lafiya gabannin babban zaben na 2023.

Bola Tinubu
Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Kashim Shettima wanda ya kasance abokin takarar Tinubu shine ya wakilce shi a taron wanda ya wakana a babban cibiyar taro na kasa da kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan nan sai hotuna suka bayyana a soshiyal midiya inda aka nuno Tinubu yana wata ganawa a UK.

Wata majiya ta kusa da dan takarar shugaban kasar ta ce Tinubu ya mayar da hankali wajen shirya manufofinsa.

Ana sanya ran tsohon gwamnan na jihar Lagas zai halarci wata muhimmiyar ganawa a Abuja a ranar Juma’a, rahoton New Telegraph.

Majiyar ta ce:

“Zai dawo kafin karshen mako.
“Yana ta hutu da aiki ne, yana ta ganawa masu muhimmanci, yana samun jawabai masu amfani da karanto takardu da kammala aiki kan manufofinsa. Yana ta ayyuka.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Dandazon Mata Suka Fito Kan Tituna Don Nuna Soyayyarsu Ga Bola Tinubu Ya Gaji Buhari a 2023

A lokacin da ake tsaka da rare-radin rashin lafiyarsa, dan takarar Shugaban kasar na APC ya saki bidiyonsa yana motsa jiki a shafinsa na Twitter.

Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranar Fara Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa

A wani labarin, mun ji cewa am’iyyar All Progressives Congress APC za ta kaddamar da yakin neman zabenta na shugaban kasa na 2023 a ranar Litinin, 10 ga watan Oktoba.

Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar da kwamitin kamfen dinta ke shirin tarbar dan takararsu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda ya tafi kasar Ingila.

Jaridar ta rahoto cewa ana sanya ran Tinubu wanda ya shafe yan kwanaki a birnin Landan zai dawo gida Najeriya a cikin wannan makon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel