Mahaifiyar Hadimin Shugaban Kasa Ta Rasu, Buhari Ya Aike da Sakon Ta'aziyya
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jajanta wa hadiminsa, Buhari Sallau, dangane da rasuwar mahaifiyarsa, Maryam Nuhammed
- Mai taimaka wa shugaban kasan kan kafafen watsa labaran zamani, Buhari Sallau, ya yi rashin mahaifiyarsa tana da shekaru 65
- A sakon ta'aziyya na musamman da ya aike masa, Buhari ya roki Allah ya gafarta mata ya sa Aljanna ta zame mata makoma
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar mai taimaka masa na kai da kai a ɓangaren kafafen watsa labaran zamani, Buhari Sallau.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa mahaifiyar Buhari Sallau, watau Maryam Muhammed, ta rasu tana da shekaru 65 a duniya.
Saƙon ta'aziyyar shugaba Buhari na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Femi Adesina, mai taimaka wa shugaban ta ɓangaren yaɗa labarai.
An yi wa sanarwar taken, "Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya jajantawa hadiminsa na Midiya, Buhari Sallau, kan rasuwar mahaifiyarsa."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A saƙon a'aziyar da ya aike wa Sallau, shugaba Buhari yace:
"Na samu labarin rasuwar mahaifiyarka cikin yanayin baƙin ciki, akwai zafi na ƙuna mutum ya rasa mahaifiya amma ya zama wajibi ka rungumi ƙaddara yadda ta zo maka."
"Kyawawan halinta ka ɗakko kake tafiyar da rayuwarka, kama daga rashin son kai a wurin aiki, maida hankali, wanda a yanzu ya kai ka matsayin dake kai.
Bayan haka shugaban ƙasa Buhari ya roki Allah maɗaukakin sarki, ya gafarta mata kurakuranta kuma ya sa Alhannatul Firdausi ta zama makoma a gareta.
A wami labarin kuma kun ji cewa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammed, Ya Yi Rashin Yayansa
Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, ya rasa babban yayansa mai suna, Bappah Muhammed ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.
Wata majiya tace Bappah ya rasu ne a wani Asibitin ƙasar Turkiyya da ba'a ambaci sunansa ba bayan fama da jinya.
Asali: Legit.ng