Yanzu-yanzu: Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammed, Ya Yi Rashin Yayansa

Yanzu-yanzu: Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammed, Ya Yi Rashin Yayansa

  • Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, ya rasa babban yayansa mai suna, Bappah Muhammed ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba
  • Wata majiya tace Bappah ya rasu ne a wani Asibitin ƙasar Turkiyya da ba'a ambaci sunansa ba bayan fama da jinya
  • A ranar Litinin da ta gabata 3 ga watan Oktoba, 2022 aka gudanar da Jana'izar mamacin kamar yadda Musulunci ya tanaza

Sanata Bala Muhammed, gwamnan jihar Bauchi na jam'iyyar PDP ya rasa babban yayansa, Bappah Muhammed.

Mamacin, Wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin Daraktan babban bankin Najeriya (CBN) kafin ya yi ritaya, ya rasu ne yana da shekaru kusan 60.

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi.
Yanzu-yanzu: Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammed, Ya Yi Rashin Yayansa Hoto: @Senbalamuhammed
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wata majiya mai kusanci da iyalan ta ce Bappah, Yeriman Duguri ya rasu ne ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba, 2022 a wani Asibitin Turkiyya.

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Faɗi Abinda Ya Faru Lokacin Marigayi Yar'Adua

Legit.ng Hausa ta gano cewa Marigayin ya tafi ya bar mata ɗaya da 'ya'ya biyar, sai kuma 'yan uwansa biyu, Adamu Muhammed, wakilin Bauchi da gwamna Bala Muhammed, ƙauran Bauchi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Bala Muhammed ya sanar da rasuwar

A halin yanzu, gwamna Muhammed, ya sanar da rasuwar ɗan uwansa a shafinsa na dandalin sada zumunta watau Facebook.

Yace:

"Innalillahi wa'inna Ilaihi raji'un, ko me ka samu ko ka rasa daga Allah ne kuma gare shi zamu koma. Yau mun wayi gari da rashin ɗan uwana kuma yayana, Alhaji Abubakar Bappah Muhammed, Yariman Duguri."
"Wannan babban rashi ne da giɓi gare mu iyalan marigayin duba da irin rayuwar sadaukar wa, gaskiya da rikon amanar da ya kwatanta. Allah ka gafarta wa Yerima, ka bamu hakurin jure rashinsa."

A wani labarin kuma Wani Fitaccen Malamin Musulunci Da Dalibansa Sun Nutse a Ambaliya a Kwara, Allah ya musu rasuwa

Kara karanta wannan

Bidiyon dan takarar shugaban kasan PDP na tikar rawa ya jawo cece-kuce a kafar Twitter

Wani shahararren Malamin Islama a jihar Kwara, Sheikh Abdulganiyu Nuraini, ya rasu sakamakon Ambaliyar ruwa.

Bayanai sun nuna cewa ruwan ya yi awon gaba da motar Malamin tare da wasu ɗalibansa biyu lokacin da zaau tsallaka wata gada a Ilorin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel