Wani Fitaccen Malamin Musulunci Da Dalibansa Sun Nutse a Ambaliya a Kwara

Wani Fitaccen Malamin Musulunci Da Dalibansa Sun Nutse a Ambaliya a Kwara

  • Wani shahararren Malamin Islama a jihar Kwara, Sheikh Abdulganiyu Nuraini, ya rasu sakamakon Ambaliyar ruwa
  • Bayanai sun nuna cewa ruwan ya yi awon gaba da motar Malamin tare da wasu ɗalibansa biyu lokacin da zaau tsallaka wata gada a Ilorin
  • Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya kaɗu da faruwar lamarin ya kuma jajanta wa iyalansa

Kwara - Fitaccen Malamin addinin Musulunci a jihar Kwara, Sheikh Abdulganiyu Nuraini, wanda aka fi sani da Alfa Gani Aboto da ɗalibansa biyu Alfa Azeez Omoekun da Alfa Nurudeen sun rasu sakamakon Ambaliya ranar Asabar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar Lahadi aka samu nasarar tsamo gawarwakinsu da Motar da suke ciki bayan ruwan ya janye.

Taswirar jihar Kwara.
Wani Fitaccen Malamin Musulunci Da Dalibansa Sun Nutse a Ambaliya a Kwara Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa Shehin Malamin da ɗalibansa na kan hanyar koma wa gida daga wurin Da'awah da suka halarta a Minna, jihar Neja yayin da ruwan ya yi gaba motarsa Toyota Yaris.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Dandazon Mata Suka Fito Kan Tituna Don Nuna Soyayyarsu Ga Bola Tinubu Ya Gaji Buhari a 2023

An tattaro cewa ruwan ya yi awon gaba da Motar Malamin yayin da yake kokarin tsallake wata gada kusa da Anguwar Harmony Estate/Kukende da ke yankin Akerebiata, Ilorin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Marigayi Shekih ya kasance ɗalibin Muftin Ilorin na farko, Marigayi Sheikh Kamaldeen Al-Adabiy, kuma shi ne shugaban ƙungiyar Ansarul Islam Society of Nigeria.

Haka zalika Alfa Gani Aboto, mahaddacin Alƙur'ani ne kuma jagora wajen horas da mahaddata a jahar Kwara.

Tuni aka kai gawarsa mahaifarsa Aboto, ƙaramar hukumar Asa da ke jihar Ranar Lahadi bayan an yi masa Sallar Jana'iza a Ilorin.

Manyan mutane sun jajanta rasuwar Malamin

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, Bukola Saraki, Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Zuku Gambari, na daga cikin manyan mutanen da suka nuna kaɗuwarsu da faruwar lamarin.

Bayan haka sun yi Ta'aziyya ga iyalan marigayi Shehin Malamin da sauran waɗanda Ibtila'in ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Bidiyon dan takarar shugaban kasan PDP na tikar rawa ya jawo cece-kuce a kafar Twitter

Ambaliyar da ta auku sakamakon matsanancin ruwan sama ta lalata gadoji, wuraren kasuwanci sannan kuma ta mamaye gine-ginen gwamnati da gidajen mutane a Kwara, ya yi ajalin rayuka da dama.

A wani labarin kuma mun tattara muku Jerin sunayen jihohi 32 na Najeriya da za a fuskanci ambaliyar ruwa a 2022

Hukumar NIHSA ta bayyana cewa, za a samu ambaliyar ruwa a kanan hukumomi 233 na jihohi 32 a fadin kasar nan har da FCT.

Daga cikin jihohin da shugaban hukumar ya ambata akwai Adamawa, Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Cross- River, Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262