'Dan Najeriya ya Maka Banki a Kotu kan N27k, An Biya Shi Diyyar Makuden Kudi

'Dan Najeriya ya Maka Banki a Kotu kan N27k, An Biya Shi Diyyar Makuden Kudi

  • Wani 'dan Najeriya mai suna Omogiade Mega Gideon ya bada labarin yadda ya maka banki a kotu bayan kasa cire N27,000 da yayi a POS
  • Gideon yace daga bisani an biya shi diyyar N150,000 daga bankin kuma an bashi wasikar bada hakuri kan abinda ya faru bayan sun yi sasanci
  • Matashin ya cigaba inda ya shawarci 'yan kasa kan abinda ya dace su yi wa bankunansu idan suna samu matsala da su

Wani 'dan Najeriya mai suna Omogaide Mega Gideon, ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda zasu shawo kan matsalolinsu da bankunansu bayan ya samu N150,000 da ya maka bankinsa a kotu.

Gideon yayi martani ne ga wata budurwa a Twitter da ta jajanta yadda aka cire mata N1.1 miliyan daga asusun bankinta ba tare da ta sani ba.

Gideon Bank
'Dan Najeriya ya Maka Banki a Kotu kan N27k, An Biya Shi Diyyar Makuden Kudi. Hoto daga @MegaGideon
Asali: Twitter

A wallafar da yayi, Gideon ya sanar da cewa ya maka bankinsa a kotu ne bayan yayi kokarin fitar da N27,000 daga POS kuma suka ki fita sannan ya ki sauraron rokon da suka yi masa.

Kara karanta wannan

Dawisun Namiji Mai Kyawawan Mata 8 Ya Ce Wasu Cikinsu Na Kishi Da Shi, Hotuna Sun Bayyana

Yace sun yanke hukuncin sasantawa ba a kotu ba bayan alkalin kotun majistaren ya roke shi kuma hakan yasa bankin suna basi N150,000 tare da wasikar ban hakuri.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Na maka @UBAGrouo a kotu kan cire N27,000 da nayi kokarin yi a POS amma ya gagara. Sun roke ni na ki hakura. Alkalin ne ya roke ni muka sasanta a tsakaninmu, bankin sun biya nin N150,000 da kuam wasikar ban hakuri.
"Ku samu lokaci da kuma banki mafi kusa, ku maka su a kotu kuma cikin wata shida ko shekara daya zasu shiga taitayinsu."

A yayin da jama'a suka dame shi da tambayoyi, ya shawarci cewa:

"Ka samu lauya, ku tattauna kan kudin shari'ar. Ka tabbatar kana da shaida inda ya dace, lauyanka zai rubutawa bankin ka wasika tare da bayanin abinda ya faru. Idan suka ki daukar mataki, maka su a kotu."

Kara karanta wannan

Ni Kadai Iyayena suka Haifa: Matar da ke da Tattaba Kunne 101 ta Bayyana Hotunansu

Soshiyal Midiya sun yi martani

@iamotistemitope tace:

"Nayi matukar jin dadin wannan labarin. Don Allah 'dan uwa ya dace ka bayyana jama'ankomai yadda zaka taimaka musu. Ka bayyana yadda lka bi dalla-dalla ta yadda jama'a zasu dinga maka bankunansu a kotu."

@Ifeoluebby yace:

"Hanyar da ake bi ba mai wuya bace kamar yadda ake tunani. Kawai ku bi abinda ya rubuta ku samu lauya. Hanyar tafi ka fara jiran sakarkarun bankunanku suna muku wulakanci."

@tintinaliza tace:

"@UBAGroup har yanzu suna rike da N25,000 dina tun ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata kuma na dinga kaiwa da kawowa inda suke cewa kudin baya bankinsu. Har yanzu wanda na turawa bai samu kudina ba ni kuma basu dawo min da shi ba."

@bentejnr yace:

"Don Allah ya zamu yi, babbar yayata an daskarar da asusun bankinta dauke da kudade masu yawa. Da farko sun fara cire N30,000 babu dalili kuma da muka yi korafi sai aka daskarar da asusun bankin."

Kara karanta wannan

Yadda DSS Ta Cafke Soja 'Mai Sayar Wa Masu Garkuwa Bindigu' A Abuja

Anambra: An Tsinta Gawar Ma'aikacin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta da ya Bace

A wani labari na daban, an tsinta gawar jami'in Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC, wanda aka bayyana batansa a jihar Anambra mai suna Duruocha Osita Joel.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, an samu gawarsa ne a kan titin Isu-Aniocha dake karamar hukumar Awka ta arewa a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel