Anambra: An Tsinta Gawar Ma'aikacin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta da ya Bace

Anambra: An Tsinta Gawar Ma'aikacin Hukumar Zabe mai Zaman Kanta da ya Bace

  • An tsinta gawar Duruocha Osita Joel, jami'in hukumar zabe mai zaman kanta da ya bace a cikin kwanakin nan
  • Kamar yadda Festus Okoye, jami'in yada labarai na INEC ya sanar, an ga gawar wurin titin Isu-Aniocha dake Awka ta arewa
  • Ya sanar da cewa na dauke gawar sannan 'yan sanda da sauran jami'an tsaro sun fara binciken silar batarsa da mutuwar

Anambra - An tsinta gawar jami'in Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC, wanda aka bayyana batansa a jihar Anambra mai suna Duruocha Osita Joel.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, an samu gawarsa ne a kan titin Isu-Aniocha dake karamar hukumar Awka ta arewa a jihar.

Duruocha babban jami'in ne mai mukamin Principal Executive Officer II a matsaki na 10.

Kara karanta wannan

An gano wata maboyar 'yan bindiga a Arewa, an fatattaki tsageru, an ceto mutanen da aka sace

Kamar yadda kwamishinan kasa na hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayarwa masu kada kuri'u kai, Festus Okoye, ya bayyana:

"A ranar Laraba, 28 ga watan Satumban 2022, sakataren gudanarwa na hukumar a jihar Anambra, Okwuonu Jude, ya bayyana batan wani jami'i mai suna Duruocha Jude, mai mukamin Principal Executive Officer II da mataki na Grade Level 10.
"A ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, sakataren gudanarwa ya kara da sanar da hukumar cewa an tsinta gawar Duruocha kan titin Isu-Aniocha-Urum dake karamar hukumar Awka ta jihar Anambra inda wasu suka yasar da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sauran ma'aikatan hukumar, 'dan uwan Duruocha da 'yan sanda sun dauke gawarsa tare da mika ta ma'adanar gawawwaki. 'Yan sanda da sauran jami'an tsaro sun fara bincike domin gano abinda ya kai ga batansa da mutuwarsa."

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

Atiku Ya Yi Magana Bayan Fallasar Wike, Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Ci Zabe A 2023

A wani labari na daban, 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya tabbatarwa mutanen Akwa Ibom cewa za a warware rikicin cikin gida na jam'iyyar nan ba da dadewa ba.

Atiku ya bada tabbacin ne a ranar Juma'a yayin da ya ke yi wa mutane a filin wasanni na Godswill Akpabio yayin bikin cikar jihar shekaru 35 da kafuwa, rahoton Vanguard.

Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Atiku ya yi kira ga yan jihar su taimakawa PDP ta kwace mulki a kasa ta kuma cigaba da mulkar jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel