Ni Kadai Iyayena suka Haifa: Matar da ke da Tattaba Kunne 101 ta Bayyana Hotunansu

Ni Kadai Iyayena suka Haifa: Matar da ke da Tattaba Kunne 101 ta Bayyana Hotunansu

  • Wata mata mai suna Marguerite Peg Koller, ta girma a Philadelphia a matsayin ‘ya daya tilo da iyayenta suka haifa
  • Yayin da take tasowa, babban burinta a lokacin kuruciya shine ta samu kanne don suyi wasa da dariya tare
  • Koda dai bata samu kanne ko daya ba, Allah ya azurta ta da yara da jikoki masu yawan gaske wadanda ke debe mata kewa

Marguerite Peg Koller ta kasance ‘ya daya tilo a wajen iyayenta kuma tana matukar son samun kanne a lokacin da take tasowa.

A cewar Marguerite, rayuwa a matsayin ‘ya daya akwai kadaici sosai kuma a kodayaushe tana addu’an Allah ya baiwa mahaifiyarta haihuwar wani dan.

Iyali
Ni Kadai Iyayena Suka Haifa: Uwa Ta Nuna Tattaba-kunnenta Guda 101 A Wasu Hadaddun Hotuna Hoto: Washington Post
Asali: UGC

A kullun ta kan fita waje wurin ‘ya’yan makwabta domin suyi wasa tare.

Tunda mafarkinta na son samun kanne bai samu ba, sai Marguerite ta fara burin tara iyali masu yawa daga gareta, lamarin da Allah ya nufi faruwarsa, The Washington Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wanka Kullum Asarar Ruwa Ne: Bidiyon Kyakyawar Budurwar da Tayi wata 1 Babu Wanka

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Allah ya amshi addu’an Marguerite

Marguerite ta samu masoyi kuma tare suka haifi yara goma sha daya wadanda suka haifa mata jikoki 56.

Yanzu haka, matar tana da tattaba kunne 101 kuma hotunan da ke nuno dukkaninsu a tare ya yadu.

Da suke magana game da yawan ahlinsu, yaran sun bayyana cewa suna alfahari da farin cikin fitowa daga irin wannan gida na musamman.

Chris Kohler mai shekaru 60 ta nuna sha’awarta ga irin so da kaunar da iyayenta ke nunawa junansu.

Ta ce:

“Suna da kyakkyawar alaka. Suna aiki tare a kasuwanci da ma gida. Suna kasancewa tare a kodayaushe, suna rike da hannun juna kodayaushe. Ina fatan cewa zan samawa kaina wani abu kamar wannan.
“Muna yan uwa maza da mata da yawa da muke wasa tare da kuma taimaka mana. Wannan na birgeni, kuma a kodayaushe ina son samun iyali mai yalwa.”

Kara karanta wannan

Mai kamar maza: Bidiyon budurwa mai tuka tirela ya girgiza intanet, jama'a sun shiga mamaki

Wanka Kullum Asarar Ruwa Ne: Bidiyon Kyakyawar Budurwar da Tayi wata 1 Babu Wanka

A wani labarin, wata budurwa da tayi ikirarin cewa ta shafe tsawon wata guda babu wanka ta haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya.

A wani bidiyo wanda ya yadu a TikTok wanda a ciki ne ta bayyana hakan, budurwar ta ce ita ta tabbatar cewa ba sai mutum yayi wanka kullun bane zai ji dadi.

Jama’a sun soki furucin nata, inda wasu da dama suka nuna shakku kan ikirarin nata kuma hakan yasa ta yin martani a sashin sharhi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel