Kakakin Majalisar Wata Jihar Arewa Ya Bayyana Yadda Yan Ta'adda Suka Saka Shi Kuka Da Zubar Da Hawaye
- Ibrahim Balarabe Abdullahi, kakakin majalisar dokokin Jihar Nasarawa ya ce yan ta'addan Darul-Salam sun saka shi zubar da hawaye
- Dan majalisar mai wakiltar Ugya/Umaisha a majalisar jihar ya furta hakan ne yayin da ya tafi ziyarar jaje a garuruwan da abin ya shafa
- Abdullahi ya ce a ranar da ya samu labarin yan ta'addan na Darul-Salam sun kai hari mazabarsa ya sako daga gadonsa ya fara zubar da hawaye kafin ya tashi ya yi alwala ya yi nafila
Nasarawa - Kakakin Majalisar Jihar Nasarawa, Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi, ya yi bayanin yadda yan ta'addan Darul-Salam suka saka shi zubar da hawaye.
Abdullahi, wanda ke wakiltar Ugya/Umaisha a jihar, ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar jaje ga garuruwan da ambaliyar ruwa ya shafa, Daily Trust ta rahoto.
Tsaffin Hotunan Gogarman Mai Garkuwa Da Mutane John Lyon Yana Bikin 'Birthday' A Cikin Banki Sun Bayyana
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce hare-haren yan ta'addan Darul-Salam ya kusa tilasta mutane dena bin hanyar Toto-Ugya-Umaisha, yana mai cewa mutane sun samu sauki bayan gwamnatin jihar ta dauki mataki.
Yadda harin yan ta'addan Darul-Salam ya saka ni kuka
Ya ce:
"Abin ya kai matsayin da mutane ba su iya bin hanyar Toto-Ugya-Umaisha saboda harin yan ta'addan Darul-Salam amma mun gode Allah yau, mutane na sun samu sauki.
"Ranar da na samu labarin yan ta'addan Darul-Salam sun kai hari mazaba ta, na sako daga gado na fara zubar da hawaye. Daga baya na tafi na yi alwala na yi sallar nafila raka'a biyu."
Abdullahi ya yi kira ga al'umma su bawa gwamnatin APC goyon baya
Kakakin majalisar ya yi kira ga mutanen jiharsa su cigaba da bawa gwamnatin APC karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule goyon baya don inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a yankin.
Ya kuma yi kira ga matasa su cigaba da zaman lafiya da bin doka da oda musamman a lokacin da aka fara harkokin zabe.
DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike
A wani rahoton, Yan sandan farin kaya na DSS na cigaba da bibiyan wadanda ke da alaka da Tukur Mamu, wanda ya taimaka wurin sulhu da yan bindiga, a yayin da suka kama surukinsa, Abdullahi Mashi, a daren ranar Alhamis.
Daily Trust ta tattaro cewa jami'an yan sandan sirrin sun kuma ziyarci gidan surukin Mamu, Ibrahim Tinja, wanda shima an kama shi an kuma dawo da shi Najeriya tare da mawallafin na Desert Herald a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng