DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike

DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike

  • Hukumar yan sandan farin kaya, DSS, ta kama Abdullahi Mashi, mahaifin matar mawallafin jaridar Desert Herald, Tukur Mamu
  • Hakan ya biyo bayan kama Mamu tare da matansa da babban dansa ne da aka yi a filin jiragen sama na Aminu Kano bayan dawo da su daga Misra
  • Rahotanni sun bayyana cewa an saki matan Mamu amma kawo yanzu shi da dansa Faisal Mamu suna tsare a hannun yan sandan na sirri

Yan sandan farin kaya na DSS na cigaba da bibiyan wadanda ke da alaka da Tukur Mamu, wanda ya taimaka wurin sulhu da yan bindiga, a yayin da suka kama surukinsa, Abdullahi Mashi, a daren ranar Alhamis.

Daily Trust ta tattaro cewa jami'an yan sandan sirrin sun kuma ziyarci gidan surukin Mamu, Ibrahim Tinja, wanda shima an kama shi an kuma dawo da shi Najeriya tare da mawallafin na Desert Herald a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mun Gano Kayan Sojoji, Makudan Kudade A Gidan Tukur Mamu, DSS

Tukur Mamu
DSS Ta Kama Mahaifin Matar Tukur Mamu A Yayin Da Ake Fadada Bincike. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama Mamu da sauran iyalansa a filin tashin jirage na Malam Aminu Kano a ranar Laraba bayan an dawo da su daga Misra bisa umurnin hukumomin tattara bayanan sirri na Najeriya.

An ce mawallafin yana kan hanyarsa na zuwa Saudiyya ne don yin Umara tare da matansa biyu da babban dansa, Faisal Mamu da surukinsa, Ibrahim Tinja.

Daily Trust ta rahoto cewa an saki matan Mamu sai dai shi kansa da dansa da kuma surukinsa har yanzu suna tsare a hannun jami'an tsaron.

Iyalin Tukur Mamu Sun Bada Labarin Yadda DSS Suka Shigo Dakin Matansa Cikin Dare

A wani rahoton, iyali da ‘yanuwan Malam Tukur Mamu sun bayyana cewa sun kidime a sakamakon shigo masu gida da hukumar DSS suka yi a garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jami'an DSS Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu, Sun Kwashe Kwamfuyutoci da Takardu

Wani ‘danuwan Malam Tukur Mamu ya shaidawa Daily Trust cewa dakarun DSS sama da 50 suka shigo gidansu cikin motoci kimanin 20 a daren Alhamis.

Jami’an tsaron na fararen kaya sun isa gidan Tukur Mamu da ke Unguwar Dosa a jihar Kaduna da kusan karfe 12:30am, a lokacin kusan kowa ya kwanta.

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel