Idan Na Zama Shugaban Kasa, Zan Tattauna Da ’Yan Aware, Babu Ruwana Da ’Yan Bindiga, Inji Peter Obi

Idan Na Zama Shugaban Kasa, Zan Tattauna Da ’Yan Aware, Babu Ruwana Da ’Yan Bindiga, Inji Peter Obi

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour ya bayyana kadan daga manufofinsa da kuma akidun da ya amince dashi
  • Ya ce abu ne mai sauki ya gana tare da tattaunawa da duk wata tawagar da ke jin bata amince da hadin kan Najeriya ba
  • Sai dai, ya ce ba zai ba da kofar tattaunawa da da 'yan bindiga saboda su tatattun 'yan ta'adda ne masu rike makamai

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour ya ce zai tattuna da 'yan aware a lokacin da 'yan Najeriya suka zabe shi don ya gaje kujerar Buhari, TheCable ta ruwaito.

Da yake magana a ranar Laraba a wata hira da gidan talabijin na Arise, Obi ya ce akwai bukatar sake fasalin Najeriya, amma sake fasalin kundin tsarin mulkin kasa zai dauki tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Zakuna sun ragewa sojoji aiki, sun hallaka wasu tarun 'yan ta'addan da suka addabi jama'a

Peter Obi ya zai iya tattaunawar sulhu da 'yan aware, amma ban da 'yan bindiga
Idan Na Zama Shugaban Kasa, Zan Tattauna Da ’Yan Aware, Babu Ruwana Da ’Yan Bindiga, Inji Peter Obi | Hoto: mrf.io
Asali: UGC

Ya bayyana cewa:

"Muna bukatar sake fasalin kasar nan, hakan alheri ne ga kasar. Sake fasali ne na kundin tsarin mulki, amma zai dauki lokaci. Akwai abu daya da ya kamata ka kula dashi. Ba ka bukatar jiran irin wannan sake fasali kafin ka cire mutane daga talauci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Don magance matsalolin tsaro, baka bukatar jiran sake fasalin kundin tsarin mulki. Irin wadannan za su faru kuma tare da amincewar dukkan kasa."

Obi ya ce ba zai zama shugaba mai tsauri ba idan ya lashe zabe, zai ke tattaunawa da jama'a don habaka ci gaban ksaar.

Kana, ya ce babu yadda za a yi ya zama shugaban kama karya a lokacin mulkin dimokradiyya.

Zan saurari 'yan aware, amma ban da 'yan bindiga

Ya ce zai saurari masu fafutukar ballewa daga Najeriya da duk wadanda suka nuna kin amincewa da hadin kan kasar saboda tabbatar da mafita ga kowace matsala a kasar, Heritage Times ta tattaro.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An fara kamfen zaben 2023, jigon APC ya ce bai san inda Tinubu yake ba

Sai dai, da aka tambaye ko zai iya tattaunar sulhu da 'yan bindiga, sai ya ce:

"Ba sa daga mutanen da zan tattauna dasu."
"'Yan bindiga 'yan bindiga ne, 'yan ta'adda 'yan ta'adda ne. Zan ji da hakan yadda ya dace."

'Yan awaren IPOB sun sha bayyana ayyukan ta'adda da suka yi a Najeriya, kana akan gansu dauke da makamai

Jam'iyyun siyasa dai sun fara gangamin kamfen a jiya Laraba 28 ga watan Satumba a shirin tallata 'yan takarar da za su gwabza a babban zaben 2023.

A jihar Filato 'yan a mutum jam'iyyar Peter Obi suka fara yawon gangaminsu a jihar Laraba.

Zan Yi Kamfen A ‘Kowane Sashe Na Najeriya’, inji Dan Takarar APC Tinubu

A wani labarin na daban, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga shirinsa na kamfen din zaben 2023, Channels Tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Bayyana Abinda Zai wa 'Yan Najeriya 100m a Fannin Lafiya Idan Ya ci Zabe

Tinubu ya ci alwashin cewa, zai taka kowane bangare a Najeriya domin tallata aniyarsa ta gaje kujerar Buhari a 2023.

A baya an yada jita-jitar cewa, akwai yiwuwar lafiyar Tinubu ta hana shi samun damar yawo a jihohin Najeriya da sunan kamfen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel