Mata Tayi Shigar Ma'aikatan Lafiya, Ta Sace Daya Daga Cikin Tagwayen da Aka Haifa a Asibiti

Mata Tayi Shigar Ma'aikatan Lafiya, Ta Sace Daya Daga Cikin Tagwayen da Aka Haifa a Asibiti

  • Rundunar 'yan sanda jihar Bauchi sun tabbatar da sace daya daga cikin tagwayen da wata mata ta haifa a asibitin ATBU a Bauchi
  • An gano cewa, matar da ta sace jinjirin tayi shigar ma'aikatan asibitin sannan ta bukaci mika jinjirin sashen shan magani
  • Mahaifiyar tagwayen tana gane an sace mata daya daga cikin yaran ta suma inda yanzu aka bazama binciko wacce ake zargin

Bauchi - An shiga tashin hankali a dakin haihuwa na asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda aka sace daya daga cikin tagwaye da aka haifa.

A zantawarsa mahaifin tagwayen da aka haifa da Daily Trust, Ibrahim Dallami Khalid ya ce wata mata ta shiga dakin da matarsa take kwance ​​da tagwayen a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Zan Iya Dukan Kirji In Rantse Cewa Mijina Bai Taba Cin Amanata ba, Jarumar Fim

Taswirar Bauchi
Mata Tayi Shigar Ma'aikatan Lafiya, Ta Sace Daya Daga Cikin Tagwayen da Aka Haifa a Asibiti. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce matar ta bayyana a matsayin jami’a a asibitin kuma ta shaida wa matarsa ​​cewa daya daga cikin tagwayen na bukatar magani a wani sashin da ke asibitin, inda ya kara da cewa mayaudariyar ta dauke jaririn har aynzu babu amo ba labari.

Khalid ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wata mata ce ta shiga cikin dakin a lokacin ziyarar, ta gaishe da dukkan majinyatan da ke wurin. Na ga matar amma ina tsammanin matata da mahaifiyarta sun san ta.

“Daga baya da na bar asibiti, matata ta ce mahaifiyarta ta kawo mata ƙwai. Yayin da take kokarin fita siyo kwai, sai matar ta sake zuwa ta tambayi surukata inda ta dosa. Ta amsa ta fita.
“Matar ta yi amfani da damar ta zauna kusa da matata, ta gaya mata cewa daya daga cikin tagwayen ba shi da lafiya kuma tana son kai jaririn wurin kulawa da jarirai na musamman.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

"Matata ta yarda ta dauki jaririn. Tun daga wannan lokacin, babu wani bayani game da inda jaririn yake. "

Da Daily Trust ta nemi jin ta bakin mahaifiyar jinjirin, Ibrahim ya ce tun da lamarin ya faru ta suma.

Shugaban Kwamitin bayar ga masana kiwon lafiya na Asibitin, Dakta Haruna Liman, ya kwatanta lamarin a matsayin wani abin takaici.

Ya ce:

“An shaida mana cewa wacce ake zargin ta kulla alaka da mara lafiyar da ‘yan uwanta da ke zaune tare da ita kuma ta sa ido sosai kan motsin su.
"Lokacin da wacce ake zargin ta zo daukar daya daga cikin jariran, mahaifiyar ta mika mata yaron da son rai kuma babu wanda ya yi zargin wani abu har sai da ta yi bayyana cewa ba a ga jaririnta ba."

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya kara da cewa an fara gudanar da bincike domin cafke wacce ko wadanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Alkawarin Aure: An Fara Gabatar da Shaidu Kan Hadiza Gabon a Kotun Shari'ar Musulunci

An Cafke Farfesan Da Ta Yi Wa Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' A Abuja, Yan Najeriya Sun Yi Martani

A wani labari na daban, 'yan sanda sun kama wata lauya kuma mai rajin kare hakkin bil adama a Abuja, Farfesa Zainab Duke Abiola, kan dukkan yar sanda mai tsaronta, Sufeta Teju Moses.

An kama Farfesan tare da yar aikinta, Rebecca Enechido, kan cewa sun duki yar sanda mai tsaron saboda ta ki yin wasu ayyukan gida da ta saka ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: