Bidiyo: Mai Garkuwa da Mutane dake Watsin Daloli a Soshiyal Midiya Yana Zubda Hawaye a Hannun 'Yan Sanda

Bidiyo: Mai Garkuwa da Mutane dake Watsin Daloli a Soshiyal Midiya Yana Zubda Hawaye a Hannun 'Yan Sanda

  • John Lyon, matashin dake watsi da daloli a soshiyal midiya tare da bayyanawa jama'a cewa guminsa ne, ya shiga hannun 'yan sanda kan zargin garkuwa da mutane
  • A bidiyon da ya bayyana, an ga Lyon yana kuka tare da rokon 'yan sanda cewa sau biyu kadai ya taba saka kungiyarsa ta sace wasu mutane aka karba kudin fansa
  • Sai dai wani mutum ya bayyana cewa ya gane fuskar Lyon tunda kungiyarsa ta taba sacesa kuma har dukan kawo wuka aka yi masa a gabansa

Bidiyon John Lyon, wanda ake zargi da kasancewa shugaban wata kungiyar garkuwa da mutane, ya bayyana yana zubda hawaye kamar karamin yaro yayin da ya shiga hannun 'yan sanda.

A wani bidiyo, wanda ake zargin da aka fi sani da Lion White, ya bayyana babu riga inda yake sanye da gajeren wando kadai a jikinsa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

John Lyon
Bidiyo: Mai Garkuwa da Mutane dake Watsin Daloli a Soshiyal Midiya Yana Zubda Hawaye a Hannun 'Yan Sanda. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ba tare da aa sanya masa ankwa a dukkan hannayensa ba, Lyon ya dinga rokon gafara inda yake cewa sau biyu kadai ya taba garkuwa da mutane, Daily Trust ta rahoto hakan.

Ya kara da rokon 'yan sandan da su taimaka su sake shi saboda matarsa ba ta dade da haihuwa ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata murya a gefe da ake zargin ta 'dan sandan mai tuhuma ce ta tambayi wanda ake zargin cewa:

"Toh kana nufin mutum biyu kadai ka sa kungiyarka ta yi garkuwa da su?"

Wanda a take Lyon ya ce:

"Eh Yallabai."

'Dan sandan ya bashi amsa da:

"Kai makaryaci ne!"

Sai dai wani mutum da yayi ikirarin cewa yana daya daga cikin wadanda Lyon ya sace, yace ya gan shi ido da ido yayin da yake hannun miyagun.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a wata jihar Arewa yayin da 'yan sanda suka kashe matashi dan shekara 16

Duk da ba a nuna fuskarsa a bidiyon ba, mutumin da ke magana da turanci mara kyau ya dinga ihu da dukkan karfin muryarsa.

"Na gan ka a daya daga cikin ranakun da aka kusa kashe ni da duka a sansaninku. Ka yi bacci a kan benci yayin da ake azabtar da ni. Idan mun je kotu, zan bayyana ka a gaban alkali."

Lyon wanda ya cigaba da kuka ya tsaya na wani lokaci inda yake cewa:

"Oga ban san komai a kan wannan lamarin ba."

Amma mutumin ya tsaya tsayin daka inda ya ce tabbas ya ga Lyon, lamarin da ya janyo tsokaci daban-daban a soshiyal midiya.

Hotuna kala-kala da bidiyoyi na rayuwar waddaka da Lyon ke yi ana tsaka da matsanancin halin da jama'a ke ciki a kasar nan sun dade suna yaduwa a soshiyal midiya.

A wani bidiyo, wanda ake zargin ya bayyana daloli inda aka ji yana cewa:

Kara karanta wannan

Na Bannatar Da Kudi N8m Wajen Shan Kwaya: Matashin Da Ya Tuba Ya Baiwa Matasa Shawara

"Kudi sun yi! Ku nemi kudi! Ku nemi kudi!! Ku nemi kudi!!!"

Akwai wasu hotunansa masu yawa a wurare daban-daban da suka hada har da otal din Transcorp dake Abuja.

Wanda ake zargin an gano cewa yana rayuwarsa ne a jihar Bayelsa inda ake ganinsa da rigunan kamfen din jam'iyyun siyasa a kasar nan.

Kotu ta Yankewa Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Abokin Harkarsa Shekaru 21 a Gidan Maza

A wani labari na daban, wata kotun laifuka na musamman dake Ikeja a jihar Legas a ranar Litinin ta yankewa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans hukunci.

Kotun ta yankewa Evans da abokin harkallarsa, Victor Aduba hukuncin shekaru 21 a gidan yari bayan garkuwa da suka yi da wani 'dan kasuwa mai suna Sylvanus Ahamonou tare da karbar $420,000 na fansa daga iyalansa, jaridar Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Alkawarin Aure: An Fara Gabatar da Shaidu Kan Hadiza Gabon a Kotun Shari'ar Musulunci

Abokin harkar Evans mai suna Victor Aduba wanda tsohon soja ne an yanka masa hukuncin shekaru 21 a gidan yari kan zargi hudu da ake masa da suka hada da garkuwa da mutane, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel