Da Duminsa: Kotu ta Yankewa Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Abokin Harkarsa Shekaru 21 a Gidan Maza

Da Duminsa: Kotu ta Yankewa Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Abokin Harkarsa Shekaru 21 a Gidan Maza

  • Wata kotun laifuka na musamman dake zama a Ikeja ta jihar Legas ta yanke hukunci kan gagarumin mai garkuwa da mutane
  • Kotun a ranar Litinin ta yanke hukuncin zaman shekaru 21 a gidan gyaran hali kan Evans da abokin harkallarsa
  • An kama su da laifin garkuwa da wani mashahurin 'dan kasuwa mai suna Sylvanus Ahamonou tare da karbar $420,000 na fansa

Legas - Wata kotun laifuka na musamman dake Ikeja a jihar Legas a ranar Litinin ta yankewa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans hukunci.

Mai Garkuwa da Mutane
Da Duminsa: Kotu ta Yankewa Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane da Abokin Harkarsa Shekaru 21 a Gidan Maza. Hoto daga tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Kotun ta yankewa Evans da abokin harkallarsa, Victor Aduba hukuncin shekaru 21 a gidan yari bayan garkuwa da suka yi da wani 'dan kasuwa mai suna Sylvanus Ahamonou tare da karbar $420,000 na fansa daga iyalansa, jaridar Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Neja, Sun Halaka Rayukan Bayin Allah

Abokin harkar Evans mai suna Victor Aduba wanda tsohon soja ne an yanka masa hukuncin shekaru 21 a gidan yari kan zargi hudu da ake masa da suka hada da garkuwa da mutane, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin yanke hukunci, Mai shari'a Oluwatoyin Taiwo tace masu gurfanarwar sun yi nasarar tabbatar da al'amarin garkuwa da mutanen da kuma mallakar makamai ga wadanda aka yankewa hukuncin, jaridar Vanguard ta rahoto.

Mai shari'a Taiwo tace:

"Pw3 ya gane wanda ake kara na farko a kotu yayin da yake bayar da shaidarsa. Ya kara da gane shi a ofishin 'yan sanda kusan watanni biyu kafin a mika lamarin gaban kotu.
"Ya tabbatar da cewa rufe masa ido aka yi kafin a mika shi bas din. Yace yana ganinsa, ya bayyana cewa wannan ne wanda yayi garkuwa da ni. Na kalla bidiyon inda wanda ake kara na farko ya bayyana shi yayi garkuwa da PW3.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotu Ta Zabi Ranar Gardama Tsakanin Gwamnati Da ASUU

"Wanda ake karar na farko ya zauna hankali kwance a kan kujera kuma babu alamar dake nuna cewa matsa masa akayi ya amsa laifinsa. Ba a yi masa barazana ba ko wata hantara. Ya saka hannu a kan takardar.
“Ya kara da sanar da cewa ya saba ballewa tare da shiga bankuna kuma daga bisani ya koma garkuwa da mutane. Na gamsu cewa wannan kotun zata iya yankewa wanda ake zargin hukunci da kalaman da ya furta na amsa laifinsa."

Alkalin ta kara da cewa babu wata hujja a gaban kotu da ta bayyana cewa 'yan sanda sun halaka yaran Evans uku.

Ta kara da yankewa Aduba hukunci kan amsa laifinsa da yayi tare da yanke cewa yayi zaman gidan yarinsa ba tare da tara ba.

Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 1, Sun Sace Manoma 3 A Kaduna

A wani labari na daban, rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da manoma uku yayin da suka kashe wani mutum daya a garin Kurgin Gabas da ke yammacin karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Taron Gangamin UN: Hotunan Da Bidiyon Shugaba Buhari Yayinda Ya Isa Birnin New York Cikin Dare

Kungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari wato BEPU ta ce tun a ranar 1 ga watan Satumba yan bindiga suka toshe babban titin Birnin-Gwari-Funtua sannan suka kwace motoci fiye da 30 ciki harda manyan motocin daukar kaya, The Nation ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel