Tinubu Zai Lashe Zaben 2023: Binciken Mujallar Economist (EIU)

Tinubu Zai Lashe Zaben 2023: Binciken Mujallar Economist (EIU)

  • Mujallar The Economist ta yi hasashen cewa dan takarar jam'iyyar APC zai lashe zaben 2023
  • Mujallar wacce ta shahara ta ce rikicin dake gudana a PDP na rage yiwuwan nasarar jam'iyyar PDP
  • INEC ta wallafa sunayen yan takara 18 da zasu yi musharaka a zaben shugaban kasan da za'a yi a Febrairun 2023

Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaben 2023, cewar Mujallar Economist Intelligence Unit (EIU).

EIU sashen leken asiri da binciken mujallar The Economist ne wanda ke da zama a Landan, kasar Birtaniya wacce ta shahara da hasashe da bincike da take wallafawa wata-wata.

Mujallar ta bayana cewa da kamar wuya dan takaran People’s Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar yayi nasara saboda rikici cikin gidan dake faruwa a jam'iyyarsa, rahoton BusinessDay.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Sun Ci Amanar Jonathan, Yanzu Abin Ya Dawo Kansu", FFK Ya Ragargaji Atiku, Saraki Da Tambuwal

Rahoton ya kara da hasashen cewa shaharar Peter Obi, dan takaran jam'iyyar Labour Party (LP), ba karamin illata PDP zai yi a yankin Kudu Maso Gabas ba.

Tinubu
Tinubu Zai Lashe Zaben 2023: Binciken Mujallar Economist (EIU) Hoto: London

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babu illar da tikitin Musulmi-Musulmi zai yiwa Tinubu

EIU ta kara da cewa da alamun tikitin Musulmi da Musulmi na Tinubu-Shettima ba zai yiwa APC wani illa ba, riwayar TheNation.

A cewar rahoton,

"Muna sa ran Tinubu zai lashe kujerar shugaban kasa, kuma abubuwan dake faruwa kwanan nan na karfafa hasashenmu."
"Babu alamun tikitin Musulmi da Musulmi zai rage kuri'un Tinubu."

Rikicin PDP

Rikicin cikin gida na kan hanyar kifar da jam'iyyar adawa a Najeriya da dan takararta a zaben 2023.

Wannan rikicin ya biyo bayan zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa.

Gwamnan jihar Rivers ya bayyana cewa shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu, ya kulla yadda aka kayar da shi a zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Hakazalika ya bukaci Iyorchia Ayu yayi murabus kuma idan ba haka shi da abokansa ba zasu goyi bayan Atiku ba.

Jerin Sunayen Gwamnoni, Tsaffin gwamnoni da, Ministoci Da Suka Yi Baran-Baran Da Kamfen Atiku

Rikicin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ya dau sabon salo yayinda manyan jiga-jiganta sukayi hannun riga da yakin neman zaben Atiku.

Jiga-jigan wanda suka yiwa kansu lakabi magoya bayan Gwamnan jihar River, Nyesom Wike, sun hadu a daren Talata a gidansa inda suka yanke shawarar baran-baran da yakin neman zabe jam'iyyar PDP.

Zaku tuna cewa Jam'iyyar PDP ta nada Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal matsyain Dirakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel