Atiku Ya Yi Nasara A Kotu Koli, An Watsi Da Karar Yunkurin Soke Takararsa Na Shugaban Kasa

Atiku Ya Yi Nasara A Kotu Koli, An Watsi Da Karar Yunkurin Soke Takararsa Na Shugaban Kasa

  • Kotun Kolin Najeriya ta yanke hukunci kan karar da aka shigar don soke zaben Atiku Abubakar
  • Alkalan kotun kolin sun ce ba su da hurumin sanya baki cikin harkokin cikin gidan jam'iyyar PDP
  • Atiku Abubakar ne ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar kuma dan Arewa ne

Abuja - Kotun Kolin ta yi watsi da karar da aka shigar kan tilastawa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP baiwa dan kudancin Najeriya takarar kujerar shugaban kasa, rahoton AIT.

Wannan ya biyo bayan karar da daya daga cikin yan takaran zaben kujerar kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar jihar Abia, Cosmos Ndukwe, ya shigar kan shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu.

Yace rashin baiwa yankin kudu tikitin takarar shugaban kasa karkashin Jam'iyyar PDP ya sabawa kundin tsarin mulkin PDP.

Kara karanta wannan

Ku Shawo Kan Matsalar Cikin Gida Kafin Ku Ceto ‘Yan Najeriya, Keyamo Ga PDP

Zaku tuna cewa uwar jam'iyyar PDP ta baiwa kowani dan yanki daman takara a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa inda Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben.

Alkalan kotun kolin sun bayyana cewa an yi watsi da karar ne saboda kotun ba tada hurumin sanya baki cikin harkokin cikin gidan jam'iyyar PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Supreme
Atiku Ya Yi Nasara A Kotu Koli, An Watsi Da Karar Yunkurin Soke Takararsa Na Shugaban Kasa
Asali: UGC

PDP Ta Yanke Shawarar Cigaba Da Harkokin Kamfenta Ko Ba Su Wike

Jam'iyyar People’s Democratic Party PDP ta bayyana cewa ba zata fasa rantsar da kwamitin yakin neman zabenta ba ranar Laraba, 28 ga watan Satumba, 2022 duk da ficewar wasu gwamnoni, tsaffin gwamnoni da manyan jiga-jigan jam'iyyar.

PDP ta bayyana cewa ba zata fasa cigaba da dukkan shirye-shiryen da tayi ba, kuma ba zata dakatar da komai ba don ficewar su Wike.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Tambuwal ya karbe mukamin shugaban gwamnonin Najeriya

Sakataren yada labaran jam'iyyar, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel