PDP Ta Yanke Shawarar Cigaba Da Harkokin Kamfenta Ko Ba Su Wike

PDP Ta Yanke Shawarar Cigaba Da Harkokin Kamfenta Ko Ba Su Wike

  • Jam'iyyar PDP ta kammala zaman gaggawar da ta shiga biyo bayan ballewar Wike da wasu jiga-jigan jam'iyyar
  • Kakakin jam'iyyar yace ko kadan ba zasu fasa yin komai ba kuma ranar Laraba za'a rantsar da kwamitin kamfe
  • Rikicin jam'iyyar adawa ta PDP ta dau sabon salo yayinda manyan jiga-jiganta sukayi hannun riga da yakin neman zaben Atiku

Abuja - Jam'iyyar People’s Democratic Party PDP ta bayyana cewa ba zata fasa rantsar da kwamitin yakin neman zabenta ba ranar Laraba, 28 ga watan Satumba, 2022 duk da ficewar wasu gwamnoni, tsaffin gwamnoni da manyan jiga-jigan jam'iyyar.

PDP ta bayyana cewa ba zata fasa cigaba da dukkan shirye-shiryen da tayi ba, kuma ba zata dakatar da komai ba don ficewar su Wike.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gobe Juma'a Zan Tona Asirin Wasu Shugabannin Jam'iyyar PDP, Nyesom Wike

Deboo
PDP Ta Yanke Shawara Cigaba Da Harkokin Kamfenta Ko Ba Su Wike Hoto: OfficialPDP
Asali: Facebook

Sakataren yada labaran jam'iyyar, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.

A cewarsa, jam'iyyar ta yanke wannan shawara ne bayan zaman gaggawan da shugabanninta suka yi ranar Laraba da Alhamis, biyo bayan ballewar wasu jiga-jiganta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayinda aka tambayesa shin za'a rantsar da majalisar yakin neman zabe kamar yadda aka shirya, Ologunaba yace:

"Zamu cigaba da dukkan shirye-shiryenmu kuma bamu da niyyar dakatawa."
"Kundin tsarin mulkin jam'iyyarmu tafi komai kuma wajibi ne muyi mata biyyaya. Saboda haka duk abinda mukayi niyyar yi zai cigaba saboda babu abinda zai sa mu fasa."

An tattaro cewa wasu manyan masu fada a ji a jam'iyyar su bada shawaran ayi watsi da su Wike, za'ayi sulhu komin daren dadewa.

Jerin Sunayen Gwamnoni, Tsaffin gwamnoni da, Ministoci Da Suka Yi Baran-Baran Da Kamfen Atiku

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Dole Ayu Ya Yi Murabus" Karin Wasu Jiga-Jigai Sun Yaudari Atiku, Sun Koma Bayan Wike

Rikicin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ya dau sabon salo yayinda manyan jiga-jiganta sukayi hannun riga da yakin neman zaben Atiku.

Jiga-jigan wanda suka yiwa kansu lakabi magoya bayan Gwamnan jihar River, Nyesom Wike, sun hadu a daren Talata a gidansa inda suka yanke shawarar baran-baran da yakin neman zabe jam'iyyar PDP.

Zaku tuna cewa Jam'iyyar PDP ta nada Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal matsyain Dirakta Janar na yakin neman zaben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel