An Cafke Farfesan Da Ta Yi Wa Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' A Abuja, Yan Najeriya Sun Yi Martani

An Cafke Farfesan Da Ta Yi Wa Yar Sanda Mai Tsaronta 'Jina-Jina' A Abuja, Yan Najeriya Sun Yi Martani

  • Rundunar yan sanda ta kama Farfesa Zainab Duke Abiola kan duka tare da raunata jami'ar yan sanda mai tsaronta a gidanta a babban birnin tarayya Abuja
  • Sufeta Janar na yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bada umurnin a gudanar da sahihin bincike tare da gurfanar da farfesan da sauran wadanda ke da hannu
  • Yan Najeriya sun fusata kan lamarin inda suka yi amfani da shafukan sada zumunta suka rika bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin da bada shawarwari na mafita

FCT, Abuja - Yan sanda sun kama wata lauya kuma mai rajin kare hakkin bil adama a Abuja, Farfesa Zainab Duke Abiola, kan dukkan yar sanda mai tsaronta, Sufeta Teju Moses.

An kama Farfesan tare da yar aikinta, Rebecca Enechido, kan cewa sun duki yar sanda mai tsaron saboda ta ki yin wasu ayyukan gida da ta saka ta.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a wata jihar Arewa yayin da 'yan sanda suka kashe matashi dan shekara 16

IGP Usman
An Kama Wata Farfesa A Abuja Kan Dukar Yar Sanda Mai Tsaronta 'Wacce Ta Ki Yin Aikin Gida'. Hoto: @daily_trust.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani faifan bidiyo da ya bazu a ranar Laraba, an ga yar sandan sanye da unifom zaune a kasa jini na fita daga jikinta, tana cewa a kai ta asibiti.

Kakakin yan sanda, CSP Muyiwa Adejobi, wanda ya tabbatar da kamun a ranar Alhamis ya ce yan sandan na neman yar aikin da aka ce tare da ita aka yi dukan.

Ya ce sufeta janar na yan sanda, Usman Alkali Baba, ya yi tir da dukan ya kuma umurci a binciki wadanda ake zargin.

Sufeta Janar na yan sanda ya yi tir da sukan da Farfesa Zainab ta yi wa yar sanda mai tsaronta

Ya ce:

"IGP ya yi tir da dukan yar sanda Sufeta Teju Moses, da mai gidanta lauya mai kare hakkin bil adama Farfesa Zainab Duke Abiola da masu aikin gidanta, wata Rebecca Enechido da wani namiji da ake nema suka yi mata.

Kara karanta wannan

Farfesa Zainab Da Mai'Aikinta Sun Lallasa 'Yar Sanda A Abuja, An Damkesu

"Zainab Duke, haifafiyar Mbaise, ta yi wa mai tsaronta rauni a tare da wasu da suka taya ta a ranar Talata 20 ga watan Satumban 2022, a gidanta da ke Garki, Abuja, saboda rashin yarda ta saba dokar aiki ta rika mata aikin gida.
"IGP ya umurci a bincike wadanda ake zargi da yanzu suke hannu, duba da cewa binciken da aka fara ya nuna akwai alamar rashin gaskiya a bangaren farfesan da yar aikinta."

Ya cigaba da cewa:

"IGP ya bukaci masu binciken su tabbatar an kamo wadanda ake zargi da suka tsere don su fuskanci doka. Yana da kyau a sani cewa ,wacce ake zargin, Farfesa Zainab, wacce ta ambaci IGP da yan gidansa, da wasu manyan yan sanda ba ta da wani alaka da yan sanda kamar yadda ake yada wa a kafafen sada zumunta."

IGP ya umurci a janye masu tsaron farfesa Zainab

Adejobi ya ce IGP ya bada umurnin a janye dukkan yan sanda masu tsaron farfesan ya kuma nuna rashin jin dadin yadda wacce ta ke ikirarin kare hakkin bil adama za ta keta hakkin wani mutum.

Kara karanta wannan

Fashin Motar Dakko Kudi: A Yafe Min, Wannan Na Ne Farko, Korarren Jami'in DSS Ya Roki Alfarma

Ga martanin wasu masu amfani da shafin Twitter:

@sunie316:

"Farfesa Zainab Duke-Abiola ta nuna yadda wasu matan ke zaluntar mata yan uwansu. Idan za ta iya yi wa yar sanda hakan, ka yi tunanin abin da za ta iya yi wa yar aikinta da ta umurci ta doki yar sandan."

@DavidGeraldjrC ya ce:

"Lokacin da Abba Kyari ya aikata laifi babu wanda ya fada mana karamar hukumarsa, yanzu saboda sunanta Zainab suna son su fayyace daga Mbaise ta fito, Don yan Najeriya su san ita Igbo ne. Wannan ya saba dokar aiki."

@aliyu_solomon:

"Mai rajin kare hakkin bil adama tana cin zarafin jami'an tsaro .... wannan rashin hankali ne."

@Ezralaah1:

"Ya kamata @policeNG su mutunta kansu su janye jami'ansu da ke tsaron fararen hula."

Asali: Legit.ng

Online view pixel