Farfesa Zainab Da Mai'Aikinta Sun Lallasa 'Yar Sanda A Abuja, An Damkesu

Farfesa Zainab Da Mai'Aikinta Sun Lallasa 'Yar Sanda A Abuja, An Damkesu

  • An damke Lauya kuma Farfesa tare da mai aikinta kan laifin lallasa dogarinta a birnin tarayya
  • Sifeto Janar na yan sanda ya yi Allah wadai da wannan mumunan abu da ya faru da jami'ar
  • IGP Usman Baba ya bada umurnin gaggauta hukunta Farfesae tare da dukkan masu hannu ciki

Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Baba, ya bada umurnin hukunta Farfesa Zainab Duke Abiola da mai'aikinta Rebbeca Enechido bisa dukan tsiya da suka yiwa wata jami'ar hukumar yan sanda, Insfekta Teji Moses.

Kakakin hukumar yan sandan Najeriya, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa tuni an damke Farfesar.

Ya ce saura mutum daya, wani namiji wanda ya gudu yanzu.

Zainab
Farfesa Zainab Da Mai'Aikinta Sun Lallasa 'Yar Sanda A Abuja, An Damkesu Hoto: Leadership
Asali: Twitter

IGP Baba ya yi Alla-wadai da wannan farfesa wacce ke ikirarin ita lauya ce kuma mai kare hakkin bil adama, cewar CSP Olumuyiwa Adejobi.

Kara karanta wannan

Wike Ya Fallasa Ayu, Ya Bayyana Babban Mukamin da Yake So Idan Atiku Ya Ci Zabe

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa Farfesa Abiola sun lallasa jami'ar ne ranar Talata, 20 ga Satumba, 2022 a gidanta dake Garki, Abuja don ta ki yi musu aikin gida.

Jaridar Leadership ta bayyana cewa Farfesa Abiola ta kasance tsohuwar matar marigayi Chief MKO Abiola.

A jawabin da ya fitar yace:

"Sifeto Janar na yan sanda ya bada umurnin janye dukkan jami'an yan sandan dake gidanta kuma yayi Alla-wadai da matar dake ikirarin mai rajin kare hakkin bil adama amma ta keta hakkin jami'ar yan sanda mai tsareta."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel