Kin yi Sa'ar Mahaifi: Budurwa ta Dauka Bidiyon Mahaifinta Yana Aikin Birkila a Ginin Gidanta

Kin yi Sa'ar Mahaifi: Budurwa ta Dauka Bidiyon Mahaifinta Yana Aikin Birkila a Ginin Gidanta

  • Wata kyakyawar budurwa ta yi bidiyon mahaifinta yana aikin birkila a filin da take ginawa don ta adana kudinta
  • Kamar yadda tace, da kan shi yace zai yi aikin kyauta saboda baya don ta kashe kudi wurin biyan masu kwadago
  • Jama’a da yawa da suka kalla bidiyon sun yi martani daban-daban inda wasu suka ce tayi sa’a da samun irin wannan mahaifin

Wata kyakyawar budurwa ta bayyana bidiyon mahaifinta yana aiki matashin birkila yana hada kasa a filin da take ginawa.

Budurwar ta bayyana cewa, mahaifinta ya yanke hukuncin yin aikin ne saboda ta adana kudadenta kada ta kashe tana biyan masu aiki.

Nifer da Babanta
Kin yi Sa'ar Mahaifi: Budurwa ta Dauka Bidiyon Mahaifinta Yana Aikin Birkila a Ginin Gidanta. Hoto daga TikTok/@hannies00
Asali: UGC

Kamar yadda budurwar tace:

“Ya ce da ni kada in bata kudina. Zai iya min a matsayina na diyarsa.”

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakyawar Budurwa Mai Aski da Tayi Wuff da Kwastoma Cike da Soyayya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalla bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

A yayin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tara sama da tsokaci 1500 tare da jinjina sama da 7000.

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama’a.

Montreal 2 yace:

"Bambi, na kasa rike hawayena, ina ma mahaifina a raye yake shima, na san cewa zai iya yi min hakan. Na mutunta mahaifinki ta yadda ya samu tsawon kwana har ya ga cigabanki."

SimaGray02 yace:

"Kina da sa'a... Ni ban san ya soyayyar uba take ba kuma duk da yana raye, amma zan tabbatar da cewa yarana sun samu irin mahaifinki."

Danny signal yace:

"A gaskiya wannan abun ya taba zuciyata, wanne irin mahaifin kirki ne wannan."

jamiecurtis56 yace:

"Mahaifin kirki kuma mai kula, Allah ya kara tsawon rai."

Kara karanta wannan

Jama'a sun sha mamakin yadda wani dan Najeriya ke tikar aikin wahala a Dubai

Da Digirina na Tafi Libya Aikin Goge-goge: Budurwa 'Yar Najeriya da ake Biya N100,000 Albashi

A wani labari na daban, wata budurwa 'yar Najeriya dake gangariyar turanci a yanar gizo ta koka kan yadda masu digiri ke barin Najeriya kuma suke kananan ayyuka a Libya.

A bidiyon budurwar, tace tana da digiri kuma tana bukatar kudi don yin rayuwa mai kyau. Ta sanar da yacca ake biyanta N25,000 a wata lokacin da take koyarwa a Najeriya.

Budurwar wacce ta lankwasa harshe zuwa ingantaccen turanci domin tabbatar da cewa digiri gareta, ta sanar da cewa tana koyar da ajujuwa shida reras.

Asali: Legit.ng

Online view pixel