Wani Dan Najeriya Ya Fito Faifan Bidiyo, Ya Nuna Sana’ar da Yake Yi a Dubai

Wani Dan Najeriya Ya Fito Faifan Bidiyo, Ya Nuna Sana’ar da Yake Yi a Dubai

  • Wani dan Najeriyan da ya tsallaka kasar Dubai ya girgiza intanet yayin da ya yada irin faman da yake a kasar
  • A wani bidiyon da ya yada, an ganshi babu riga yana share zufa, inda yake yake aikin facin tayar mota
  • Yayin da wasu suka yaba da kokarinsa da kuma nuna gaskiyarsa da hanyar da yake neman kudi, wasu kuma sun tsorata da tsallakawa kasashen waje

Cece-kucen jama'a ya mamaye wani bidiyon da aka yada a intanet na wani matashi dan Najeriya dake nuna sana'ar da yake a Najeriya.

Wannan lamari na matashi ya ba mutane da dama mamaki, ganin yadda birnin Dubai ya kai iyakar birni amma ake samun aiki irin wannan a madadin aiki mai gwabi.

Bidiyon da aka gani a TikTok, mutumin da ba a san sunansa ba ya bayyana sana'ar da yake yi. Ya dai yi aikin ne a cikin bidiyon ba tare da furta kalma ko daya ba.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: An kai makura, dalibai sun toshe hanyar filin jirgin sama suna zanga-zanga

Bidiyo ya nuna yadda matashi ke aikin wahala a Dubai
Wani Dan Najeriya Ya Fito Faifan Bidiyo, Ya Nuna Sana’ar da Yake Yi a Dubai | Hoto: TikTok/@yungmoney149
Asali: UGC

His manual work involves tyres. In the clip, he used much physical strength as he folded a tyre into a bigger one.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aikin nasa ya shafi facin tayun mota da hannu. A bidiyon an ga yana amfani da hannayensa wajen daidaita wata tayar mota.

Yana dai aikinsa kamar ba komai ba, amma da zai yi amfani da karafan da aka yi na musamman don aiki da ya samu sauki.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

Lucky onyemaeme Chig tace:

"Ba zan taba yin wannan ba, har abada, sai ka tsufa jikinka zai gaya maka.

Mc Daniel yace:

"Na gwammace na koma gida."

Benjamin Stewart yace:

"Amma kuma hakan ya maka?"

chibuzoraj yace:

"Yadda kake nade taya anan UAE akwai wahala, idan da zan nuna maka yadda zan yi da za ka gane yadda yake da sauki."

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar shan kebura, wani yaro ya zubarwa mahaifiyarsa manjan N4k, ya damalmale jikinsa

Rebby yace:

"Abin da zan iya cewa kawai shine; Allah ya albarkace ka da arziki ta aikinka na hannu. Amin."

piuskosy yace:

"Amma dai ya kamata ace suna da injinan da za su taimaka wajen kwalmada tayun."

userek9ouete90 yace:

"Yanzu a haka wani zai ta fushi dashi don ba ya turo kudi."

Budurwa Ta Kammala Digiri, Ya Sha Alwashin Rushe Gidansu Na Kasa Sannan Ta Gyara Shi

A wani labarin, wata matashiyar da ta kammala karatunta na digiri ta ba da mamaki a kafar sada zumunta yayin da dauki hoto a gaban wata bukka da tace gidansu ne.

Sai dai, budurwar bata zo da wasa ba, domin kuwa ta sha alwashin sauya wannan gidan bukka ya zama katafaren gida, lamarin da ya girgiza jama'a.

Mujallar Squad ce ta yada wannan hoton a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel