Bidiyon Kyakyawar Budurwa Mai Aski da Tayi Wuff da Kwastoma Cike da Soyayya

Bidiyon Kyakyawar Budurwa Mai Aski da Tayi Wuff da Kwastoma Cike da Soyayya

  • Wata kyakyawar budurwa mai sana’ar aski a Owerri, jihar Imo ta auri kwastomanta dake zuwa aski
  • Kamar yadda bidiyon da ta wallafa a TikTok ya nuna, soyayyar ya fara ne bayan ta yi wa matashin aski kuma suka kulla abokantaka
  • Abokantakarsu ta cigaba inda tayi kamari har suka fara soyayya da ta kai su aure cike da murna

‘Yan Najeriya a TikTok suna shagalin murnar auren wata kyakyawar budurwa mai aski wacce tayi wuff da daya daga cikin kwastomominta.

A wani bidiyo mai taba zuciya wanda budurwar ta saka a TikTok, budurwar mai suna Her Royal Majesty, tace abokantakarsu ta fara ne bayan ta yi masa aski.

Saurayi da budurwa
Bidiyon Kyakyawar Budurwa Mai Aski da Tayi Wuff da Kwastoma Cike da Soyayya Hoto: TikTok@herroyalmajesty00.
Asali: UGC

Daga kwastoma zuwa mijin aure

Mai askin wacce take zama a Owerri, jihar Imo tace sun zama abokai ne da farko kafin su fara soyayya.

Kara karanta wannan

Kin yi Sa'ar Mahaifi: Budurwa ta Dauka Bidiyon Mahaifinta Yana Aikin Birkila a Ginin Gidanta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bayyane yake cewa babu abinda zai iya raba su a yanzu tunda sun yo aure.

Ta wallafa bidiyoyin aurensu. A daya daga cikin bidiyoyin da ya wallafa, ita ce da kanta ta yi wa angonta aski da safiyar auren wurin karfe 5 na asuba.

Her Royal Majesty ta bayyana cewa mijinta ne kwastomanta da tafi so.

Kalla bidiyon a kasa:

‘Yan TikTok sun yi martani

Tuni ‘yan TikTok suka dinga tururuwa suna martani kan labarin soyayyarsu.

Ga wasu daga cikin martanin:

@lady_aiibee tace:

“Na yi miki murna.”

@Sochima Ikechukwu yace:

“Na taya ki murna! A gaskiya zan fara aski. Akwai karin bayani ne?”

Amarya Ta Saka Kawayenta 100 A Dandalin WhatsApp, Ta Dorawa Kowannensu Harajin N5k Na Shagalin Bikinta

A wani labarin, wata mai shirin zama amarya ta nemi gudunmawar kudi daga wajen kawayenta kimanin su 100 gabannin bikin aurenta.

Kara karanta wannan

Da Digirina na Tafi Libya Aikin Goge-goge: Budurwa 'Yar Najeriya da ake Biya N100,000 Albashi

Matashiyar ta saka kawayen nata a wani shafi kan WhatsAPP sannan ta wajabta masu biyan akalla N5k kowannensu don bikinta.

Yusuf Bolaji wacce ta fallasa hirar a kan Twitter ta bayyana cewa N5k da kowannensu zai na daban ne baya ga sauran kudade da za a kashe da kuma biya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel