Da Digirina na Tafi Libya Aikin Goge-goge: Budurwa 'Yar Najeriya da ake Biya N100,000 Albashi

Da Digirina na Tafi Libya Aikin Goge-goge: Budurwa 'Yar Najeriya da ake Biya N100,000 Albashi

  • Wata budurwa 'yar Najeriya wacce ta kammala digirinta ta tafi kasar Libya inda ta zama mai goge-goge saboda ana biyanta N25,000 a Najeriya
  • Budurwar tace tana alfahari da aikin share-sharen da take yi wanda ake biyanta zunzurutun kudi har N100,000 duk wata
  • 'Yan Najeriya tuni suka dinga martani kan bidiyonta tare da cewa sun yi sha'awar yadda take alfahari da aikinta kuma take neman na kanta

Wata budurwa 'yar Najeriya dake gangariyar turanci a yanar gizo ta koka kan yadda masu digiri ke barin Najeriya kuma suke kananan ayyuka a Libya.

A bidiyon budurwar, tace tana da digiri kuma tana bukatar kudi don yin rayuwa mai kyau. Ta sanar da yacca ake biyanta N25,000 a wata lokacin da take koyarwa a Najeriya.

Budurwa a Libya
Da Digirina na Tafi Libya Aikin Goge-goge: Budurwa 'Yar Najeriya da ake Biya N100,000 Albashi. Hoto daga TikTok/@bintsirajj
Asali: UGC

Na koyar da Jss 1 zuwa SS 3

Kara karanta wannan

Amarya Ta Saka Kawayenta 100 A Dandalin WhatsApp, Ta Dorawa Kowannensu Harajin N5k Na Shagalin Bikinta

Budurwar wacce ta lankwasa harshe zuwa ingantaccen turanci domin tabbatar da cewa digiri gareta, ta sanar da cewa tana koyar da ajujuwa shida reras.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda tace, ita ke shirya abinda zata koyar da daliban a kullum kafin ta samu wannan albashin mai bada takaici.

Ba nan aka tsaya ba, tace ana biyanta N25,000 duk wata kuma tana koyar da JSS 1 zuwa SS 3, hakan ne yasa aikin ke cigaba da bata wuya.

Tace gara ta karba aikin kazanta da ta karba tsaftatacce wanda ake biyanta kalilan.

A kalamanta:

"Kun san irin wuyar shi kuwa? Kun san abubuwa nawa nake shiryawa wanda zan koyar kafin watan ya kara?"

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin martanin jama'a.

Toyah x yace:

"Ina lafahari da ke, kudinki halastattu ne kuma masu tsafta kuma ina farin ciki yadda baki ji kunyar yin aikin ba. Ubangiji zai budo miki wanda ya fi hakan."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta haramtawa 'yan Najeriya cin gandan fatar dabbobi, ta fadi dalilai

Abdul wahab yace:

"Na so yadda ki ke fitar da kalamanki. Gwanin sha'awa da Yarabanci, Turanci da Larabci. Duk ke kadai 'yar uwa."

Dav pat yace:

"A gaskiya turancinki ya tafi da ni."

Bidiyon Macen Farko 'Yar Najeriya da ta Siyawa Kanta Iphone 14 Pro Max da Guminta Ya Janyo Cece-kuce

A wani labari na daban, wata budurwa ‘yar Najeriya ta bar jama’a baki bude bayan ta wallafa bidiyon kanta da IPhone 14 Pro Max da ta siya da kudinta.

A bidiyon da ta fitar, ta bayyana yadda ta je shagon siyar da waya domin siyawa kanta. Daya daga cikin ma’aikatan shagon ya bukaci ta bude wayar don ya gani.

Budurwar 'yar Najeriya tace duk da ta siya wayar da kudinta da ta adana, tana matukar farin ciki da mallakarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel