Yanzu-Yanzu: Wani Gwamnan Arewa Ya Kamu da Rashin Lafiya, An Masa Tiyata

Yanzu-Yanzu: Wani Gwamnan Arewa Ya Kamu da Rashin Lafiya, An Masa Tiyata

  • Likitoci sun yiwa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom tiyata amma kuma yana cikin koshin lafiya
  • Kakakin gwamnan, Terver Akase, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba
  • Akase ya ce maruru ne ya fitowa ubangidan nasa a goshi don haka aka yi masa tiyata kuma an sa filastan ne don hana kwayoyin cuta shiga

Benue- Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an yiwa gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom tiyata.

Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin labarai, Terver Akase, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba.

A yan kwanakin da suka gabata, ana ta cece-kuce kan batun lafiyar Ortom bayan bayyanar hotunansa dauke da filasta a kai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Nada Kwarrren Dan Jarida Matsayin Sabon Shugaban NTA Na Kasa

Wasu yan kasa sun bukaci ayi masu bayani domin kore duk wani shakkunsu game da rade-radin da ake yi kan lafiyar gwamnan.

Da yake martani, Akase ya ce ya zama dole a kore irin wannan jita-jitan yayin da ya yi bayanin cewa lafiyar gwamnan ba abun damuwa bane.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wasu mutane sun yi tambayoyi game da filastan da ke manne a goshin Gwamna Samuel Ortom a yan kwanakin da suka gabata.
“A matsayinsa na gwamna wanda lafiyarsa abun damuwa ne ga mutanensa, yana da kyau mu sanar da mutanen Benue game da huldarsa, lafiya da shige da ficensa a kodayaushe.
“Kamar kowani dan adam, wani maruru ya fitowa Gwamna Ortom a gefen goshinsa na dama kuma an yi masa tiyata. Filastan da aka saka don hana kwayoyin cuta shiga ne. ba wani babban abu da za a damu bane.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnoni, tsaffin ministoci, jiga-jigai masu goyon bayan Wike sun yi hannun riga da kwamitin kamfen PDP

“Muna masu godiya da dukka kiraye-kirayen waya da tambayoyi daga mutanen jihar Benue masu karamci. Gwamna Ortom na cikin koshin lafiya kuma ya ci gaba da gudanar da harkokinsa, daya daga ciki shine na kaddamar da masaukin Aper-Aku da mukaddashin shugaban kungiyar ammintattu na PDP, Adolphus Wabara , ya sake ginawa a Benue Peoples House, Makurdi."

'Yan Najeriya Sun Kai Wuya, Zasu Ba Wasu 'Yan Takara Mamaki A 2023, Gwamna

A wani labari na daban, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun gaji da gwamnati a dukkan matakai, yana mai gargadin cewa masu zabe zasu ba yan siyasa da jam’iyyun siyasa mamaki a babban zaben 2023 mai zuwa.

Da yake zantawa da manema labarai a Benin, babban birnin jihar Edo, a ranar Talata, Obaseki ya ce yakamata yan siyasa su yi tsammanin abun mamaki daga masu zabe saboda rashin shugabanci mai kyau da kuma iya aiki, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: An cimma matsaya tsakanin ASUU da majalisa, za a kai batu gaban Buhari kafin a koma makaranta

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel