'Yan Najeriya Sun Kai Wuya, Zasu Ba Wasu 'Yan Takara Mamaki A 2023, Gwamna

'Yan Najeriya Sun Kai Wuya, Zasu Ba Wasu 'Yan Takara Mamaki A 2023, Gwamna

  • Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya magantu a kan abun da zai faru da yan siyasa da jam'iyyun siyasa gabannin zaben 2023
  • Obaseki ya ce lallai 'yan Najeriya sun kai iya wuya kuma za su shayar da masu neman takara mamaki a zabe mai zuwa
  • Gwamnan ya ce a yanzu babu wata siyasa da za ta iya bugar kirjin cewa za ta yi nasara a zaben 2023 saboda gwamnati ta gaza a dukkan matakai

Edo - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun gaji da gwamnati a dukkan matakai, yana mai gargadin cewa masu zabe zasu ba yan siyasa da jam’iyyun siyasa mamaki a babban zaben 2023 mai zuwa.

Da yake zantawa da manema labarai a Benin, babban birnin jihar Edo, a ranar Talata, Obaseki ya ce yakamata yan siyasa su yi tsammanin abun mamaki daga masu zabe saboda rashin shugabanci mai kyau da kuma iya aiki, Daily Trust ta rahoto.

Obaseki
'Yan Najeriya Sun Kai Wuya, Zasu Ba Wasu 'Yan Takara Mamaki a 2023, Gwamna Hoto: The Bridge News
Asali: UGC

Obaseki ya ce:

“’Yan Najeriya sun gaji da rashin aiki da gazawar jami’an gwamnati da sauran wakilai kuma za su yi watsi da hakan idan ba a dauki mataki don sauya lamarin ba. Babu jam’iyyar siyasa a yau da za ta iya bugan kirjinta sannan sun ce za su lashe zabe ko tabbacin nasara a zabe mai zuwa a kasar nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mutane na kallo kuma dalili daya da zai za mutane su bar gidajensu zuwa wajen zabe shine saboda akwai dalili imma na zaben wani ko akasin haka. Idan basu amfana ba, akwai yiwuwar za su fito a ranar zabe.”

A cewarsa, mutane na bibiyar lamuran siyasa a kasar nan kuma sun shirya ba jam’iyyun siyasa mamaki.

Ya kara da cewa:

“A garemu a matsayinmu na gwamnati da wakilan mutanenmu, za mu dunga illata kanmu idan muka yi biris da sauyin da ke zuwa sannan muka yarda cewa har yanzu abubuwa suna yadda suke. Duk za mu sha mamaki kamar yadda muka fara gani. Yanzu mutane sun fara gano cewa suna bukatar gabatar da Karin bukatu daga mutanen da ke gwamnati da wadanda ke kula da arziki da dukiyoyinsu; mutane za su fita su zabi zabinsu ko ra’ayoyinsu.

“Mun yi sa’a a jihar Edo saboda mun hango zuwan haka kuma mun yi tanadi amma kalubalenmu shi ne mutane da yawa ba su yarda da hakan ba, suna tunanin muna da lokaci kuma har yanzu abubuwa za su faru kamar yadda suka saba.”

Sai dai kuma, ya yi kira ga shugabannin siyasa da su tashi tsaye domin rage radadin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Bayan Karewar Wa'adi, Wani Sanata Ya Fallasa Matakin da Suke Kan Shirin Tsige Shugaba Buhari

A wani labarin, shugaban masu tsawatarwa a Majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa yan majalisar dokokin tarayya sun dawo daga rakiyar neman a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kalu ya jadadda cewa matsalar rashin tsaro wacce ita ce ta asassa kira ga tsige Shugaban kasar ta inganta sosai, Leadership ta rahoto.

A tuna cewa wasu sanatoci a fadin jam’iyya mai mulki da mai adawa sun ba Shugaba Buhari wa’adin makonni shida ya magance matsalar rashin tsaro ko a tsige shi daga kan kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel