Buhari Ya Nada Kwarrren Dan Jarida Matsayin Sabon Shugaban NTA Na Kasa

Buhari Ya Nada Kwarrren Dan Jarida Matsayin Sabon Shugaban NTA Na Kasa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da nadin Salihu Abdulhamid a matsayin sabon direkta janar na NTA
  • Ministan Labarai da Al'adu, Mr Lai Mohammed ne ya sanar da nadin Dembos, a safiyar ranar Laraba, 21 ga watan Satumba
  • Kafin nadinsa, Dembos ne shugaban sashin kasuwanci na NTA kuma ya shafe kimanin shekaru 20 yana aiki a kafafen watsa labarai

FCT Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nada Mr Salihu Dembos a matsayin direkta-janar/babban shugaba na Gida Talabijin Na Najeriya, NTA.

Ministan Sadarwa da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, The Punch ta rahoto.

Buhari
Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Gidan Talabijin Na Kasa NTA. Hoto: Fadar Shugaban Kasa.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Wani Ministan Ya Ci Alfarmar Buhari, Ya Samu Sarauta Mai Daraja a Masarautar Daura

Ya ce nadin da aka masa na tsawon shekaru uku ne a karon farko.

Wanene Salihu Dembos, wanda Buhari ya nada mukami?

Kafin nadinsa, Mr Dembos ne babban direktan sashin kasuwanci na NTA.

Mr Dembos ya shafe kimanin shekaru 20 yana aiki a bangare kafafen watsa labarai.

Ya yi aiki a matsayin janar manaja a gidajen NTA biyu a Lokoja da Kano; kuma ya yi aiki a matsayin direkta na NTA a shiyyar Kaduna da wasu wuraren.

An Haifa Wa Matashin Hadimin Buhari Yarsa Ta Farko, Yan Najeriya Suna Ta Taya Shi Murna

Yan Najeriya sun fara tura sakonnin taya murna ga hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad da matarsa Naeemag, bisa haihuwar yarsu.

Ahmad, ya sanar a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba, cewa an haifa masa ya mace, da ya rada wa suna Fatima Bashir Ahmad.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyyar Kwankwaso Yace Likimo Tinubu Zai Dunga Yi A Bakin Aiki Idan Ya Zama Shugaban Kasa

Hadimin shugaban kasar ya bayyana murnarsa na zama mahaifi yayin da ya yi addu'ar Allah ya raya masa yarsa.

Buhari Ya Kawo Gagarumin Cigaba A Bangaren Samar Da Wutar Lantarki A Najeriya, In Ji Femi Adesina

A wani rahoton, Gwamnatin Tarayya a daren ranar Talata ta ce wutar lantarki ta inganta a karkashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari matuka idan aka kwatanta da yadda ta ke a shekarun baya.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV.

Adesina ya ce kwantiragin da gwamnatin tarayya ta yi da kamfain Siemens ne yasa ake kawo transifoma da wasu kayan lantarki don magance matsalar dauke wuta a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel