Jonathan: Abin Da Ya Sa Na Kira Buhari a Waya Kafin a Gama Kirga Kuri’un 2015

Jonathan: Abin Da Ya Sa Na Kira Buhari a Waya Kafin a Gama Kirga Kuri’un 2015

  • Goodluck Ebele Jonathan ya dauko labarin kiran wayan da ya yi wa Muhammadu Buhari ana tsakar zaben 2015
  • Tsohon shugaban kasar yace ya kira abokin takararsa a lokacin ne saboda al’ummar Najeriya su zauna lafiya
  • Jonathan da Abdussalami Abubakar sun ja-kunnen ‘yan siyasan yau da cewa burinsu ya biyo bayan kishin-kasa

Abuja - Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya tuno da abin da ya faru a zaben 2015, wanda ake ganin ya ceci al’ummar kasa a lokacin.

This Day ta rahoto Dr. Goodluck Ebele Jonathan yana bayanin abin da ya say a dauki waya, ya rangadawa Muhammadu Buhari kira bayan zaben 2015.

Shugaban kasar na wancan lokaci ya kira shugaba Muhammadu Buhari mai jiran gado domin taya shi murna, alhali ba a gama tattara kuri’un zabe ba.

Kara karanta wannan

Inyamuri ba zai gaji Buhari ba, gwamnan yankin Kudu ya bayyana dalilai

Tsohon shugaban ya yi jawabi ne a wajen wani taron zaman lafiya da aka shirya domi jin rawar da zabe ke takawa a kasa irin Najeriya mai kabilu iri-iri.

Jonathan ya hana rikici ya barke

Mai girma Goodluck Jonathan yake cewa ya kira abokin kararwarsa watau Buhari a lokacin ne domin ya ceci mutanen Najeriya, kuma hakan ne ya faru.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Saboda haka Jonathan wanda ya yi mulki na tsawon shekaru biyar tsakanin 2010 da 2015 ya yi kira ga ‘yan siyasar da suke neman mulki a zaben 2023.

Jonathan
Goodluck Jonathan a Bamako Hoto: @GEJonathan
Asali: Twitter

Dr. Jonathan ya bada shawara cewa dole ‘yan takara su bi a sannu da burinsu, su sa kishin kasa a gaba, wannan zai zaunar da kasar cikin zaman lafiya.

Kiran Janar Abdussalami Abubakar

Rahoton da muka samu yace tsohon shugaban kasa, Janar Abdussalami Abubakar (mai ritaya), ya yi makamancin wannan kira da yake jawabi a taron.

Kara karanta wannan

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

Abdussalami Abubakar yace dole ne ‘yan siyasa su sa kishin kasa a gaba, kafin burin da suke da shi, yace sai kasa ta zauna lafiya sannan za a iya mulki.

Bayansa ne aka ji Boss Mustapha wanda shi ne sakataren gwamnatin tarayya yana kokawa da siyasar da ake yi yau a Najeriya ta rashin manufa da akida.

A jawabinsa, Bishof Matthew Kukah yace ana bukatar shugabannin da jama’a za su yarda da su.

Tsohon shugaban ECOWAS, Mohammed Ibn Chambas da gwamnan Edo, Godwin Obaseki, sun bada shawarwari ga masu zabe da masu tsayawa zaben.

Jonathan da zaben 2023

Kwanakin baya kun ji kungiyoyi irinsu The APC Watchdog sun yi ta rade-radin cewa ana shirin dawo da Goodluck Ebele Jonathan kan mulki a zaben 2023.

Shugaban The APC Watchdog na kasa, Alhaji Wahab Adewale, yace ana yunkurin ba Jonathan tikiti a APC, a karshe dai hakan ta tabbata karya ce kurum.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu, Atiku Abubakar Ya Fara Tattara Sunayen Wadanda Zai Ba Mukamai

Asali: Legit.ng

Online view pixel