Hotunan Fasto Yana Raba Wa Almajirai Allo Da Kayan Karatu A Kaduna Don Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya

Hotunan Fasto Yana Raba Wa Almajirai Allo Da Kayan Karatu A Kaduna Don Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya

  • Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry a Kaduna ta raba wa almajirai alluna da kayan rubutu a Kaduna
  • Shugaban cocin, Yohanna Buru, ya ce shi da mabiyansa sun yi wannan karamcin ne don hadin kai, zaman lafiya da karfafa fahimtar juna tsakanin addinai
  • Buru ya yi wannan karamcin ne yayin da ake bikin zaman lafiya na kasa da kasa, ranar 21 ga watan Satumba ya kuma yi kira ga FG ta tallafawa ilimin almajirai

Kaduna - A wani kokari karfafa hadin kai da zaman lafiya tsakanin addinai, cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry ta raba wa dalibai alluna fiye da 100 a makaratun almajirai a Kaduna.

Yayin da ya jagoraci mambobin cocinsa a ranar Talata, Yohanna Buru, shugaban cocin, ya ce sun yi wannan karamcin ne don koyar da zaman lafiya, hakuri da addinai, da yan uwantaka tsakanin musulmi da kirista a jihar, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Yajin ASUU: An kai makura, dalibai sun toshe hanyar filin jirgin sama suna zanga-zanga

Faston Kaduna
Hotunan Fasto Yana Raba Wa Almajirai Allo Da Kayan Karatu A Kaduna Don Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya yi hakan ne a yayin da duniya ke cikin ranar kasa da kasa ta zaman lafiya a ranar 21 ga watan Satumba a yayin da Najeriya ke fama da rashin tsaro da wasu kallubalen

A cewar Buru, cocin ta shafe kwanaki uku tana rabon allunan da wasu kayan koyarwa da suka hada da alkallami da wasu kayan rubutu da karatu na harshen arabiya.

Fasto A Kaduna
Hotunan Fasto Yana Raba Wa Almajirai Allo Da Kayan Karatu A Kaduna Don Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Daga cikin unguwannin da aka yi rabon kayan karatun sun hada da Rigasa, Mando, Tudun Wada da wasu sassan karamar hukumar Igabi na jihar.

Ya ce:

"Cocin ba za ta manta da abin da wata musulma mace, Hajiya Ramatu Tijjani, ta yi ba na raba mana Bible fiye da 50.
"Wannan matar kuma ta raba zannuwa, tufafi da wasu kayan abinci ga mata kiristoci da mazajensu suka don bikin Kirsimeti da sabuwar shekara."

Kara karanta wannan

Fasto da mabiyansa sun sha bulala yayin da wasu tsageru suka farmaki coci a jihar Arewa

A yayin da ya yi kira ga shugabanni addini su mayar da hankali wurin ganin sun samar da zaman lafiya da hadin kai, ya ce wannan shine karo na biyar da cocin ke raba wa makarantun almajirai kayan karatu da rubutu.

Ya yi kira ga UNESCO, UNICEF da gwamnatin tarayya ta tallafawa ilimin almajirai a Najeriya.

Lawal Maduru, jagoran al'umma a Tudun Wada, ya yaba wa kokarin faston, yana mai cewa karamcin da ya yi nada alaka da inganta zaman lafiya, hadin kai da fahimtar juna tsakanin musulmi da kirista.

Babban Sallah: Coci A Kaduna Ta Raba Abinci Ga Musulmi Mabukata Da Marayu, Ta Yi Rabon Kudin 'Barka Da Sallah'

A wani rahoton, wani coci mai suna The Christ Evangelical and Life Intervention Fellowship Ministry ta raba abinci ga musulmi mabukata da marayu don murnar babban sallah.

Cocin ta kuma ce ta bada kyautan kudi na "Barka da Sallah" ga yara domin karfafa dankon zumunci tsakanin musulmi da kirista a jihar, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

Asali: Legit.ng

Online view pixel